Daga Ahmed Muh’d Danasabe,
Kungiyar Mafarauta ta Najeriya (HGN) a Jihar Kogi ta ceto mutane 19 da aka yi garkuwa da su, inda kuma suka kama masu satar jama’a su shida a mahadar Kabba (Kabba Junction) dake yankin karamar hukumar Adabi biyo bayan wani samame da mafarautan suka kai maboyar masu satar jama’ar.
Shugaban kungiyar ta HGN,Mallam Inusa Bature, a yayin da yake zantawa da wakilimmu ,yace ana danganta wadanda ake zargin da satar jama’a data auku kwanan nan a yankin.
“Mun samu labarin cewa anyi garkuwa da wasu matafiya, nan da nan muka hada kanmu inda muka afkawa wajen da lamarin ta faru, kuma muka yi ta arangama da batagarin
Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu,mai suna Mista Magaji Francis, yace suna kan tafiya ne daga Legas zuwa Adamawa,suna kaiwa dai dai Kabba Junction, sai kawai masu garkuwa da jama’ar suka tsayar da motarsu,inda yan bindigar suka yi garkuwa da hudu daga cikin fasinjojin,a yayin da kuma suka saki direban motar da wasu fasinjojin.
“Sun kwace mana wayoyin salularmu bayan sun kira yan uwanmu inda suka bukaci a biyasu kudaden fansa har naira miliyan 50.” inji shi.
Ya cigaba da bayanin cewa masu garkuwa da jama’ar, wadanda fulani ne,sun lakada musu duka da adda tare da azzabtar dasu da yunwa da da daure su da kuma yi musu barazanar kashe su idan har yan uwansu suka gagara biyan kudaden fansar.
“Mun gode wa Allah da kuma kungiyar mafarauta ta HGN a bisa ceto rayukanmu.” inji Mista Francis.
Wata mace wacce ita ma ta kasance daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da ita kuma ta shafe kwanaki uku a hannun masu garkuwa da jama’ar, mai suna Akanji Saidu ta bayyana cewa “muna kan hanyarmu ta zuwa Adamawa daga birnin Legas, kwatsam,sai masu garkuwa da jama’ar suka yi garkuwa damu da misalin karfe uku na safe a Kabba Junction dake babban hanyar Lokoja zuwa Okene, inda suka amshi kudade da wayoyinmu.
“Sun daddaure mu, inda kuma suka rika dukan mazajen dake cikinmu tare da jikkata biyar daga cikinsu, wadanda a yanzu suna kwance a asibitin Alheri dake Kabba Junction suna karbar magani,” in ji ta.
Daya daga cikin masu garkuwa da mutanen,ya bayyana wa wakilimmu cewa wani fulani mai suna Oga da kuma wani wai shi Yellow ne suka gayyace shi ya shiga harkar garkuwa da jama’ar.
“Mu goma sha biyu ne muka saci mutanen,inda muka karbi naira 1.5 a matsayin kudin fansa kafin mu shiga komar kungiyar mafarauta ta HGN.” Inji shi.
Shugaban karamar hukumar Adabi dake jihar Kogi, Hon Joseph Omasa Salami,wanda ya ziyarci wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa dasun a asibitin Alheri dake Kabba Junction, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da tausayi.
Ya kuma yi zargin cewa fulani dake zaune a yankin ne ke gayyatar batagari zuwa yankin,inda kuma ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki.
Daga nan Hon Salami ya yaba wa kungiyar mafarauta ta HGN da sauran jami’an tsaro a bisa kokarinsu na dakile ayyukan laifufuka a yankin.
Kayayakin da aka gano daga hannun masu garkuwa da jama’ar sun hada da bindigogin roba guda biyu da kakin sojoji da kuma wayoyin salula guda takwas.