Batun fyade a cikin al’umma ya zama sai addua, iyaye suna cikin tashin hankali dangane da yawaitar faruwar fyade dake faruwa a kodayaushe cikin al’umma. Wannan batu abu ne da ke bukatar sa ido da taka tsan-tsan. A kullum kwanan duniya ana samun sabon labari ga me da faruwar fyade, shin ta ina matsalar ta ke ne? Me yake jawo karuwar samun fyade a kullum?
Ba wani dalili da za a ce shi ne dalilin faruwar fyade a kullum sai rashin tsoron Allah, da kuma bin maganan bokaye, a mafi aksari mutane kan biyewa irin wadannan mutane don neman biyan bukata wanda a karshe abin baya kyau.
Ina Mafita
Mafita a nan ita ce :
1: Iyaye su zama masu kula da shiga da fitan yaransu.
2: kar su yadda da yaran makota ko ta unguwa suke fita da yaransu.
3: A duk lokacin da yara zasu fita a tabbatar da sunyi fita ta mutunci.
4: kar iyaye suke barin yara mata da samari kawai su kadaita a cikin gida.
5: kar a bar yara mata tafiya ta barin gari da maza su kadai komai kusancinsu.
6: Iyaye su kula wurin irin bikin da yaransu mata zasu halarta.
7: Iyaye su daina barin yara mata fita aika da dare.
8: iyaye su yawaita yi wa yara addu’a da neman tsari daga sharrin shaidan.
SHAWARA
Shawara ga iyaye mata a nan mu sa ni wannan fyade ta zama kalubale a garemu, yana da kyau mu tsaya tsayin daka da addua da kuma sa ido akan rayuwar yaranmu, kasancewar wannan zamani batun fyade ya zama innallilahi wa inna ilahi rajiun! A duniya duka babu wata uwa da zata so ace yau anyi wa ‘yarta fyade, don haka yana da kyau musan da irin mutanen da muke tare da su a makota ko cikin unguwa. Kar mu sake mu kyale su shige shige gidajen makota ko wurin da ba and aike su ba tare da idni ba.
Mu sa ni fyade mugun tabo ne da ba ya gogewa a zuciyar wacce aka yiwa har abada, haka duk uwar da ta wayi gari anyi wa yarinyar ta fyade had abada baza ta manta da hakan ba. Mu tsaya sosai don ganin mun samawa yaranmu da mu kanmu farinciki na har abada don ganin mun karesu daga sharrin afkuwar fyade. Farincikin duk wata uwa shi ne samun farincikin yaranta, mu gasgata hakan cikin kowanne yanayi.
Sister Iyami Jalo Turaki