Magajin Garin Rano Da Walin Rano Sun Sha Alwashin Ciyar Da Masarautar Gaba

Rano

Daga Mustapha Ibrahim Kano

 

A ranar Juma’a da ta gabata Majalisar masarautar Rano karkashin shugabancin mai martaba sarkin Rano Alhaji kabiru Muhammad Inuwa ta nada hakimai domin taimakawa masarautar wajen cigabanta wanda suka hada da magajin garin Rano, Honarabul Adda’u Isa Rano tsohon dan majalissar wakilai mai wakiltar Rano Kibiya da Bunkure a matsayin Magajin Garin Rano, sai Alhaji Danlami Al-hassan Rano a matsayin walin rano.

Sauran su ne Dakta Yahaya Isa Bunkure, a matsayin makaman Rano a yayin da aka nada Honarabul Al-hassan Ado Doguwa amtsayin Sardaunan Rano, RT. Kabiru Al-hassan Rurum a matsayin Turakin Rano.

A jawabinsa ga manema labarai Honarabul Ada’u Isa Rano ya bayyana cewa abin da Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi na kir-kiro masarautar Rano da sauran masarautu biyar na Kano da kuma sahalewa mai martaba Sarkin Rano nada su a wadannan mukamai a wannan lokaci abin a yaba ne kuma ya nuna gwamnan Kano mai son cigaban al’umma ce da tarihinsu a kowanne lokaci.

Har’ila yau magajin garin Rano Honarabul Ada’u ya bayyana farin cikinsa da nada shi wannan mukami na magajin garin Rano wanda ya bayyana sarautar a matsayin sarauta mai dinbun tarihi, kuma zai yi amfani da ita wajen wayar da kan al’ummar wannan masarauta wajen a fahimci abubuwan da za su kawo cigaban zaman lafiya da karuwar tattalin arziki, tsaro da ci gaba ta kowanne fanni a wannan masarauta, inda ya bayyana mai martaba Sarkin Rano a matsayin jagoran cigaban al’umma.

Shi ma ana sa bangaren, Walin Rano ya ce wannan sarauta ta Walin Rano babbar kalubale ce a gareshi na a tashi tsaye wajen ciyar da wannan masarauta gaba, domin wannan karramawa ce daga gwamnan Kano da Mai martaba Sarkin Rano ya sa aka bashi wannan sarauta, dama sauran hakimai da aka nada a wannan rana.

Alhaji Idi Gwangwan ya ce Rano ta samu jagorori da hakimai hazikai da za su ciyar da ita gaba, da Nijeriya baki daya.

 

Exit mobile version