Maganar Monguno Ta Daba Wa Nijeriya Wuka

Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Jumaa. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addua Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.
Maganar Monguno a kan makamai kamar ya tona wa Nijeriya asiri a lokachin da kasar take fama da matsalolin tsaro. Maganarsa za ta ba wa yan ta’adda karfi ne kawai, domin karfin makami shi ne karfin gwmnati, misali: kamar akuyar da aka rufa mata fatar kura, sai wani ya zo ya bude ta. Su kuwa wadanda ake zargi gwamnati ba za ta yi musu komai ba. Allah ya bamu zaman lafiya baki daya.
Sako daga Khalid Abubakar

07039631828

“Tattaunawa Da Abduljabbar Ita Ce Maslaha
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU Jumaa. Barkan ku da aiki, ina muku fatan Allah ya kara muku kwazo amin. Ina kuma muku addua Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasa wannan jarida mai farin jini baki daya.
Asali ra’ayin malaman da mai girma gwamnan Jihar Kano ya zauna da su kafin daukar matakin dakatar da Abduljabbar daga karatukansa masu shirin tayar da mummunar rigimar addini a Jihar Kano, da ma Arewacin Nijeriya matsayar malaman ita ce, kar a zauna da Abduljabbar, saboda ra’ayoyin nasa ba su da kimar da za a zauna a kansu. kari da cewa malaman sun gamsu da cewa shi wannan mutumi ba shi da ilimi da tarbiyyar da za a zauna da shi, saboda kasancewar wadannan abubuwa guda biyu rukunai ne a tattaunawar ilimi a addini. Kai, hasali ma wasu daga cikin malamai suna da shakku a kan cikar hankalin shi wanda za a zauna da shi din.
Kuma wannan ra’ayi shi ne matsayar wadanda aka ji ta bakinsu daga karshe, cikin manyan baki da aka gayyata don sa ido a kan yadda zaman zai gudana. Kamar kungiyar Jama’atu Nasril Islam, karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi da kuma Shaikh Muhammad Sani Yahya Jingir, mai jagorantar daya bangaren kungiyar Izala. Kuma da ma tun tuni wannan shi ne matsayar Shaikh Muhammad Aminu Daurawa.
Ko shakka babu wannar matsaya tana da kyau matuka, kuma abin lura ce. Saboda ba a tattaunawa da mai halayya irin ta Abduljabbar.
Amma sai dai kuma a daya bangaren an samu wasu cikin manyan malamai wadanda suka gamsu da muhimmancin yin zama da Abduljabbar din, don suna ganin dakatar da shi kadai daga yada barnarsa ba tare da an titsiye shi, an tona asirinsa wa al’umma ba, tamkar an kashe maciji ne amma ba a sare kansa ba. Saboda akwai mutane masu yawa da suka rudu da shi, akwai wasu da ya jefa musu shakku, to don a tsamar da wadannan mutane daga wannan hali da suke ciki, akwai bukatar a titsiye Abduljabbar, ya nuna inda wadannan munanan maganganu da ya danganta su ga Manzon Allah (saw) suke a cikin littatafan addinin Musulunci. Duk da cewa, kowa ya san ba a cikin littatafan suke ba, amma akwai bukatar a ritsa shi a kure jahilcinsa.
Wannan shi ne fahimtar Babban malamin hadisin nan Shaikh Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo da sauran malaman da tun tuni sun tisa Abduljabbar din a gaba, irin su Dr. Muhammad Rabi’u Umar R/Lemo da Ustaz Kabir Bashir Abdulhameed, wanda ake masa inkiya da “Hayaki fidda na kogo”.
Kuma wannan shi ne fahimtar wasu malamai da suke gefe, amma suna bibiyan lamarin, irin su Shaikh Dr. Idris Abdul’azeez Bauchi da sauransu.
Ko shakka babu za a ga wannan ra’ayi shi ma yana da karfin gaske, saboda ya wajaba a kure ramin karya a bainar jama’a, duk da cewa da ma kurarre ne.
Kuma da ma shi ma Abduljabbar din ya bukaci gwamnati ta shirya zama da shi din. Duk da cewa, daga farko da ya tashi mayar da martani a kan matakin da gwamnati ta dauka a kansa, sai ya yi maganganu na nuna fito-na-fito da gwamnatin ta Jihar Kano har mai girma gwamna ya yi masa martani mai zafi. To daga nan ne Abduljabbar ya canza salon magana.
Ala ayyi halin, ni dai ra’ayina shi ne, tun da gwamnati ta amince da maganar shirya zama kuma har shirye-shirye sun yi nisa, yin zaman nan shi ne maslaha ko shakka babu idan aka ki yi to ba a lura da janibin matsalar da wadanda suka rudu da Abduljabbar suke ciki ba. Alhali kamata ya yi a kashe maciji, a sare kansa. Muna fatan a ce, a gudanar da wannan zama a ranar Lahadin sati na sama, kamar yadda aka tsara, don a jefar da kwallon mangoro a huta da kuda.
Sako daga Aliyu Muhammed Sani.

“dan Arewa Mai Bada Kanshi, Shi Ya Sa ‘Yan Kudu Suka Raina Mu”
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMAA. Hakika mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da sakon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran alummar kasa. Muna muku adduar Allah ya kara muku hikima da basirar aiki da kuma bunkasar wannan jarida mai farin jini baki daya.
Yanzu ana nan ana fitarwa da nama zuwa Kudacin kasar nan. Ni na rasa abin da ke damun dan Arewa, kullum kuka kake cewar ba a samar maka ‘yanci, yanzu kuma ana kokarin samar maka ‘yanci kana ruguza yancin da kanka.
‘Yan Arewa sai yaushe zamu waye mu farga mu tashi daga barcin da muke domin nemar ma kanmu ‘yanci da martaba, idan har bamu tashi mun zage damtse ba, to tabbas yan Kudu za su kara gane cewar mu sakarkaru ne. Kun ga kuwa dole su rinka mana duk wulakancin da suka ga dama. Allah ya bamu ikon gyarawa.
Sako daga Mahmud Sani, KD 08151693170

Exit mobile version