Suga:
Ki hada Sugar da Almond oil ko Zaitun ko man Kwakwa da ruwan Lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan ki shiga wanka.
Ruwan Dankali
Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki shafa ruwan a inda Nankarwar take idan ya bushe za ki ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko Zaitun ko man kwakwa.
- Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
- Nijeriya Ta Yi Rashin Ɗan Kishin Ƙasa Mai Gaskiya Da Nagarta — Osinbajo
Man Kade:
Yawan shafa man kade a wurin ma yana rage ta sosai.
Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zarar sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ne babu Kemikal a cikinsa don haka yana daukar lokaci kafin a ga canji kamar, sati biyu idan ba ki ga canji ba sai ki dauki wani kuma.
Allah shi ne masani. Allah yasa mu dace.
Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba
Hanya ta 1: Dankalin Hausa
Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antiodidant. Haka kuma dankali yana dauke da sinadarin bitamin C, potassium, thiamin, riboflabin, iron, zinc da sauran su.
Yanda ake amfani da shi:
A yanka Dankali sannan a shafa a hankali a kan Nankarwar. Sai a bar shi na tsawon mintuna 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. A maimaita haka a kullum
Hanya ta 2: Alo bera
Ruwan da ke cikin Alo bera yana dauke da sinadarin Collagen wanda aka san shi da gyara fatar da ta lalace da kuma kara laushin ta, kyanta da kuma yarintar ta.
Yanda ake amfani da shi:
A karya itacen Alo bera guda sai a shafa ruwan a kan Nankarwa. A bar shi tsawon awa 2 zuwa uku sai a wanke da ruwa. A maimata hakan a kullum har sai an samu sakamako mai kyau.
Hanya ta 3: Man kadanya da koko Bota
Hadin man kadanya da koko Bota yana dauke da sinadarin bitamin E da kuma sinadaran da ke hana fata lalacewa
Yadda ake amfani da shi
Za’a samu Koko Bota karamin cokali 2, da man kadanya shima karamin cokali 2, sai sinadarin Bitamin E karamin cokali 1. Za’a narka man kadanya da kuma man koko Bota sai a kara bitamin E din a ciki a gauraya. Za’a dura gaba daya a cikin mazubi a ajiye ana shafawa a kan Nankarwar kullum.














