Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Maganta Matsalar Tsaro: Na Ci Alwashin Cika Wa Buhari Burinsa – Magashi

by
2 years ago
in MANYAN LABARAI
1 min read
Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 23 Zuwa Alhamis 26 Ga Shawwal 1441, Bayan Hijira
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ministar Harkokin Tsaro a Nijeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya), ya ce, ya ci alwashin cika wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari babban burinsa na tabbatar da cewa, gwamnatinsa ta kawo karshen matsalar tsaro a fadin tarayyar kasar.

Bayanin hakan ya na kunshe ne a cikin sanarwar da ministan ya bayar mai dauke da sa hannun mai taimaka ma sa kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadir, a Abuja yayin cikarsa shekara daya a matsayin minista, ya na mai cewa, zai yi hakan ne kasancewar Buhari a matsayin Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya, wanda ya sadaukar da kansa ga kasar ba tare da son kai ko kasala ba.

Janar Magashi ya kuma gode wa Shugaba Buhari bisa damar da ya ba shi ta bauta wa kasarsa ta haihuwa, ya na mai cewa, yanzu ne ma su ka fara aiki tukuru ga Nijeriya da ’yan Nijeriya.

Labarai Masu Nasaba

Birtaniya Ta Kwato Dala Miliyan 23 Da Ake Zargin Marigayi Abacha Ya Sha Kwana Da Su

Barazanar Da Kilisar Matasa Ke Ci Gaba Da Yi A Kano

A yayin da ya ke tabbatar da irin goyon bayan da Shugaban Kasar ya ke bai wa rundunonin sojan kasar, don kawo karshen matsalolin tsaron da su ka shafi na ’yan tayar da kayar baya, satar mutane da garkuwa da su da kuma ’yan bindiga, Janar Magashi ya bayyana kwarin gwiwarsa da cewa, lallai haske na nan tafe a karshen al’amarin.

Daga nan sai ya yi kira ga dukkan Shugabannin Rundunonin Tsaron Nijeriya da su sake tashi tsaye wajen nuna kishin kasarsu, ya na mai karawa da kiran su da su rika yin aiki tare, domin nauyi ne wanda ya rataya a wuyan dukkan ’yan Nijeriya.

A karshe ya gode wa sojojin kasar da kuma dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin tsaron Nijeriya bisa irin goyon bayan da su ke ba shi a tsawon kwanaki 365 da ya kwashe a ofis.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Neja Ta Yaba Wa Jagorancin Sarkin Musulmi Yayin Cikarsa Shekara 64

Next Post

Birnin Chongqing Ya Dauki Matakai Da Dama Na Inganta Muhallin Zama

Labarai Masu Nasaba

Birtaniya Ta Kwato Dala Miliyan 23 Da Ake Zargin Marigayi Abacha Ya Sha Kwana Da Su

Birtaniya Ta Kwato Dala Miliyan 23 Da Ake Zargin Marigayi Abacha Ya Sha Kwana Da Su

by Leadership Hausa
1 week ago
0

...

Kilisa

Barazanar Da Kilisar Matasa Ke Ci Gaba Da Yi A Kano

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 weeks ago
0

...

NSCDC

‘Yansanda Sun Lakada Wa Kwamadan NSCDC Na Jihar Imo Duka

by Khalid Idris Doya
2 weeks ago
0

...

Bana

A Shirye-shiryen Karamar Sallar Bana…

by Abdullahi Muh'd Sheka and Bello Hamza
2 weeks ago
0

...

Next Post
Birnin Chongqing Ya Dauki Matakai Da Dama Na Inganta Muhallin Zama

Birnin Chongqing Ya Dauki Matakai Da Dama Na Inganta Muhallin Zama

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: