Wani magidanci ya sari tsohuwar matarsa da ke dauke da juna biyu tare
da yayanta jim kadan bayan fitowarsu daga Babbar Kotun Shari’ar
Musulunci da ke karamar hukumar Rano a Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata, bayan da matar ta
shigar da kara kotu aka raba auren nasu da mijin nata.
Matar mai suna Shafa’atu Sale, mazauniyar garin Unguwar Kara ce a
karamar hukumar Rano, ta bayyana cewa, fitowarsu ke da wuya daga kotu
ne bayan Alkali ya raba aurensu da mijin nata mai suna Biliya
Abdullahi, sai kawai ji ta yi ya rufe ta da sara ita da yayanta mai
suna Ado Sale.
“Alkalin Kotun ya ce, na ba shi sadakinsa Naira dubu ashirin, amma sai
ya ki karba, sai Alkali ya karba a hannun Ado.
“Bayan mun fito daga kotun ne, tsohon maigidan nawa ya rika bin mu,
daga bisani kuma ya zaro wuka ya fara caka wa Ado a cikinsa, sannan ni
ma ya dawo kaina yana caka min,” a cewar matar.
Shi ma yayan nata Ado Sale ya bayyana cewa, bayan an sallame su daga
kotun ne sai ya biyo su ta baya, inda ya caka min wukar a cikina da
sauran sassan jikina.
“Da kyar na ruga da gudu zuwa bakin kotun, ban yi zaton ita ma zai
caka mata wukar ba, dga nan ne kuma sai ‘yan sanda suka zo suka cafke
shi da kyar domin kuwa har sai da suka harba bindiga,” a cewar tasa.
‘Yan sanda na cigaba da binciken lamarin wanda da zarar sun kammala za
su gabatar da shi a gaban kuliya.