A yanzu haka rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Legas na binciken wani mutum mai shekaru 42, Dabid Idibie, akan kisan matarsa, Juliana Idibie a gidansu da ke titin Joado, Oke Ira Nla, Ajah na yankin Legas.
An bayyana cewa, marigayiyar, Juliana da mijinta Dabid sun samu wani husuma mai zafi akan wasu matsalolin auren su, kuma a cikin hakan, sai ta fadi sumammiya kuma ta samu mummunan rauni a kai, a ranar 16 ga Fabrairu 2021 da misalin karfe 10 na dare.
Yayin da take kwance a cikin jininta, mijin da ke cikin fushi ya ki ceton ta har sai da ta mutu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas CSP Adejobi Olumuyiwa ya ce, jami’in dan sanda da ke aiki a sashin Langbasa, Ajah, wanda makwabcin ma’auratan ne ya sanar da shi mummunan lamarin, ya ruga da gudu zuwa wurin, ya kama wanda ake zargin sannan ya kwashe gawar zuwa dakin ajiyar gawa na asibiti.
Odumosu ya bayar da umarnin a mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar, Panti, Yaba, don gudanar da bincike na gaskiya. Yayin da yake sake nanata rashin yarda da laifuka da aikata laifuka, musamman rikicin cikin gida, CP Hakeem Odumosu yana gargadin ma’aurata da su magance duk wani sabani da rikice-rikice a koda yaushe tare da kyawawan halaye, saboda doka za ta saurarawa duk wanda ya kashe matarsa ko mata ta kashe mijinta ba.
Yana jajantawa dangi da abokai na marigayiyar game da rashin lokacin nata. CP Hakeem Odumosu ya yi alkawarin tabbatar da an yi adalci a lamarin.