Yusuf Shuaibu" />

Magidanci Ya Yanke Jiki Ya Mutu Wajen Yi Wa Iyalinsa Cefane

Wani mutumi da ba a tabbatar da sunansa ya yanke jiki ya fadi a babbar kasuwar Igbudu da ke garin Warri ta karamar hukumar Warri ta Kudu a Jihar Delta, inda kuma ya mutu nan take har lahira.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, da misalin karfe 9 na safiyar Laraba ne mutumin ya tafi kasuwar da nufin sayayyar kayan abinci da kayan miya a lokacin da ajalinsa ya tarar da shi a can.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa: “Mutumin ya tafi kasuwar ce domin sayen kayan abinci, bayan ya sayi su tumatir da tarugu sai ya nemi inda zai sayi kifi danye, a nan wani mutumi ya nuna masa inda ake sayar da danyen kifi.

“Ya nufi inda ake sayar da danyen kifin kenan sai ya yanke jiki ya fadi nan take ya mutu, mai yiwuwa ne mutumin ya mutu ne sakamakon yunwa, saboda ko daga tafiyarsa ya yi kama da mutumin da ya kwashe tsawon kwanaki bai ci abinci ba.” Inji shi. Amma ko da aka tuntubi hukumar ‘Yan Sandan Jihar Delta domin jin ta bakinsu game da lamarin, sai jami’in dake magana da yawunta, Onome Onobwakpoyeya ya ce tabbas lamarin ya auku. “Da gaske ne, amma ba mu san abin da ya yi sanadiyyar ajalinsa ba, saboda mu ba likitoci bane, mutumin ya dai yanke jiki ya fadi ya mutu kawai.” Inji shi.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi kira ga gwamnatoci, kungiyoyin addinai, kamfanoni masu zaman kansu da kuma masu hannu da shuni da su mayar da hankali wajen tallafa wa jama’a da kayan abinci. Gwamnan ya bayyana haka ne a garin Ado Ekiti ta bakin mai magana da yawunsa, Lere Olayinka, inda ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su dauki shawararsa da muhimmanci.

A cewar tsohon gwamnan, yunwa ta fi Coronabirus kashe ‘yan Nijeriya, kuma ta fi kisa cikin sauri. Sa’annan ya kara da cewa za’a yi fama da matsalolin tattalin arziki da ire irensu a sanadiyyar bullar Coronabirus, don haka yanzu ne ya kamata shugabanni su tashi tsaye su nuna jagoranci nagari ga al’ummarsu.

Exit mobile version