Yusuf Shuaibu" />

Magidanta Sun Samu Biliyan N44.62 Daga Tallafin Korona – Rahoton CBN

Rubutun Ajami

Magidanta sun sami naira biliyan 44.62 daga cikin kudaden tallafin cutar Korona daga karshen watan Nuwamba, kamar yadda alkalumar da aka samo daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana.

A cikin rahoton tattalin arziki na Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya bayyana cewa, an samu karin naira biliyan 35.43 a cikin kudaden tallafin na wata Yuli.
Daga cikin rahoton, “bankin zai ci gaba da bayar da gudummuwa wajen inganta tallalin arziki ta hanyar bayar da basuka da bunkasa samarwa da duk wasu abubuwa da ke janyo matsaloli sa harkokin wajen samarwa da kuma rarrabawa.
“Dallai wannan shirin na samar sa basuka ya yi matukar karuwa wanda ya janyo karuwar rarraba wa magidanta kudade masu yawa.
“Hukumar NIRSAL wacce take tallafa wa kananan kasuwanci ta kara yawan kudaden da kuma yawan masu amsar bashin.
“Jimillar yawan kudade na naira biliyan 44.62 aka rarraba wa magidanta a ranar 12 ga watan Nuwambar shekarar 2020, idan aka kwatantashi da na ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2020, wanda aka samu yawan magidanta masu neman zuba jari da cutar Korona ta durkusar da su.
“Hakazalika, yawan kudaden da aka bai wa kananan kasuwanci a ranar 12 ga watan Nuwambar shekarar 2020 ya kai na naira 30.90, wanda idan aka kwatanta da na ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2020 na naira biliyan 11.4, an samu karuwar masu zuba jari a cikin harkokin kasuwanci wadanda suka sami matsala lokacin cutar Korona.”
Bankin CBN a cikin watan Oktobar shekarar 2020, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ya samar da shirin tallafa wa matan karkara, wanda ake tsammanin za a bai wa mata 700,000 naira 20,000 ga kowacce mace, domin rage radadin cutar Korona a gidajen da ke yankunan karkara. Bayan haka kuma, mata guda 150,000 suka sami wannan tallafi a karkashin shirin bunkasa matan yankunan karkara a jihohi 36 da ke fadin tarayya ciki har da Babban Birnin tarayya Abuja. Ana tsammanin wadanda suka amfana da wannan tallafi ya su yi amfani da kudaden wajen gudanar da ayyukan tattalin arziki a yankunansu, domin inganta rayuwarsu wajen samun samar karuwar inganta kudaden shiga.
Bugu da kari, gwamnatin tarayya ta karkashin ma’aikatan matasa da bunkasa wasanni ta kaddamar da shirin bayar da horo a bangaren kasuwanci, domin bunkasa rayuwar matasa wajen rage yawan marasa ayyukan yi a Nijeriya.

Exit mobile version