Magoya Bayan Atiku 10,000 Sun Koma PDP A Katsina

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Shugaban Gidaunaiyar Atiku Abubakar (Atiku Care Foundation) Ghali T. Yusuf ya ce mun karbi magoya bayan tsohun mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) dubu goma daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina.

Shugaban Gidauniyar Ghali T Yusuf ya yi wanna ikirarin ne a lokacin da suka kaddamar da shuwagabanin kananan hukumomi 34 na gidauniyar a babban ofishin jam’iyyar PDP a Katsina.

Kamar yadda ya bayyana  kungiya ta shigo da mabiya jamiyyah APC wadanda suka kona Tsintsiya suka dawo PDP har su Dubu Goma 10,000 inda shugaban Atiku CareFoundation Ghali T Yusuf Ya mika rijistarsu ga shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Honarabul Salisu Yusuf Majigiri.

Daga nan sai shugaban jam’iyyar ya bada tabbacin za a mika rijistar ta su zuwa ga shuwagabin mazabunsu tare da hada su da shugwagabanin jam’iyyar na kowace mazaba domin fara aikin yakin neman zaban wazirin Adamawas.

Ghali T Yusuf ya kara da cewa kofa a bude take ga dukkanin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP tun daga Dankama har Damari domin kara amsar ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka da sha’awar komawa jam’iyyar PDP tare da bada gudunmawa ga nasarar Atiku Abubakar.

Ya kara bada tabbacin cewa wannan gidauniya ba ta wani ba ce, an kafa ta ne domin bada dukkanin gudunmawar da ta da ce da kuma tallata dan takara  domin tunkarar zabe mai zuwa ba tare da nuna wani banbanci ba.

‘’Abinda yasa Atiku care Foundation ta yi zarra a dukkanin  kungiyoyin  na PDP masu Tallata Atiku shine, Saboda jajircewar matasa hazikai da ta ke da su a jam’iyyar PDP da kuma janyo ‘yan APC cikin tafia PDP nasara, kuma muna bada tabbacin yi wa kowa adalci awannan tafiya’’ in Ghali T Yusuf

 

Ghali T Yusuf Ya ce sun riga sun kammala dukkanin shirye-shirye domin hada wani gangami na biyu domin amsar wasu mashahuran ‘yan jam’iyyar APC zuwa PDP domin tallata manufofin Atiku Abubakar wasu daga yankin Funtuwa wasu kuma daga yankin  Daura tare da wasu daga yankin Katsina.

Haka ya bayyana cewa gudauniyar Atiku Abubakar bata fidda wani  dan takara ba kuma duk wanda  ya sami tikitin jamiyyar PDP to da shi  gidauniyarAtiku za ta yi aiki, saboda haka a yanzu kowa na tane.

‘’Idan jama’a za su tuna mai girma Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa) masoyin Jamiyyah PDP ne Kuma masoyin Najeiriya ne, don haka yana tare da masoyan PDP kuma hadimi ne so sai, sannan ya shirya domin taimakon ‘yan Najeriya’’. Inji shi.

Haka kuma gidauniyar Atiku Abubakar shi ne ba zata lamuncewa duk wani da zai kawo rudani acikin wannan tafiya ta  PDP, ba kuma wanda zai ci mutuncin wani a wannan tafiya, kuma ya kamata a gane aikin wannan gidauniya shi ne tallata dan takara da kuma nemawa masa jama’a.

Exit mobile version