Magoya Bayan Inter Milan Sun Karyata Siffanta Lukaku Da Biri

Kungiyar Magoya Bayan Inter Milan ta ce, kukan birin da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Cagliari suka yi wa dan wasan kungiyar, Romelu Lukaku, wani nau’i ne na girmama shi amma ba cin zarafin sa ba.

Sanarwar da kungiyar magoya bayan ta fitar, ta ce, masoya kwallon kafa a Italiya ba sa nuna wariyar launin fata, sannan cin zarafin da aka yi wa Lukaku na cikin wasa kuma hakan tana yawan kasancewa a kasar ta Italiya.

A cewar sanarwar, magoya bayan Cagliari na fargabar kwarewar Lukaku ta jefa kwallaye a ragarsu, abinda ya sa suka fara yin kukan biri domin daburta masa lissafi a yayinda yake shirin buga fanaritin da aka bai wa Inter Milan.

Koda yake kungiyar ta bai wa Lukaku hakuri kan cin zarafin, tana mai jaddada masa cewa, Italiya ba kamar sauran kasashen Turai ba ne da ke fama da matsalar wariyar launin fata kuma zasuyi bincike akai.

Lukaku wanda ya koma Inter Milan daga Manchester United, ya jefa kwallon da ta bai wa kungiyarsa nasara da ci 2-1 a yayin wasan nasu da Cagliari kuma itace kwallo ta biyu daya ciwa kungiyar tun bayan komawarsa a watan daya gabata.

Sai dai kociyan kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, Antonio Conte, ya bayyana cewa yakamata hukumomi a kasar ta Italiya su dauki mataki mai tsauri akan masu nuna wariyar launin fata kuma akwai bukatar karantar da mutanen kasar sanin darajar kowanne dan adam.

Exit mobile version