Kwamitin bincike dake bincikar mai rikon mukamin Shugaban Hukumar Yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ibrahim Magu, ya maida hankaline kan wasu zarge-zargen da ake yi masa musamman wadanda ke da alaka da karkatar da kudade da kadarori da Hukumar ta kwato.

Lauyan Mista Magu, Wahab Shittu a cikin wata sanarwa da ya yi da gidan talabijin na Channels ya ce hukumar ta EFCC karkashin kulawar Mista Magu ba tai barna ko sakaci da kudaden da ta bankado ko ta kwato wa Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ba. Lauyan yana mai bayyana irin wadannan labaran a zaman karya.
Ya bayyana cewa sama da naira miliyan 329 da hukumar ta EFCC ta kwato an mayar dasu kai tsaye a cikin asusun ajiya na kamfanin NNPC ta hanyar remita a karkashin wata yar jejeniya ta musamman wanda kamfanin mai na kasa (NNPC), EFCC, da kuma ‘yan kasuwar NNPC suka sa wa hannu.

Lauyan ya kara da cewa za a iya tabbatar da zuwan kudaden asusun NNPC daga EFCC ta hanyar bin labaran remita, sannan kuma wannan batun ma na NNPC, kwamitin shugaban kasa dake bincikar magu bai tattauna komai akan batun ba.