Connect with us

LABARAI

Magu Ya Caccaki Lauyoyi A Kan Naira Biliyan 1.7 Da Suke Karba Na Kare Masu Laifi

Published

on

Mukaddashin shugaban hukumar hana cin hanci da karban rashawa, EFCC, Mista Ibrahim Magu ya ce, wasu manyan Lauyoyi na kasar nan suna yin zagon kasa ga yakin hana cin hanci da rashawa da ake fafatawa da shi a kasar nan, ta hanyar taimaka wa masu laifi sanin hanyar da za su bi su kubutar da kansu da gangan.
Ba tare da ya ambaci sunan kowa ba, Magu ya ce, akwai wani babban Lauyan da ya karbi Naira bilyan 1.7 daga wani mahandamin dan siyasa, a matsayin kudin ladansa na tsaya masa da ya yi a shari’ar cin hanci da ake zarginsa da ci, ba tare da Lauyan ya nu na ko gezau ba.
Ya ce, wannan dai babban Lauyan ya kuma karban tsabar Naira milyan 300 daga hannun wani gwamnan da ya fito daga kudu maso kudancin kasar nan a matsayin ladan tsaya masa da ya yi a kan daukaka karar shari’arsa, duk da hakan kuma ya kasa ya biya harajin kudaden, amma nan da nan sai ya boye a bayan shirin nan na gwamnatin tarayya na afuwar wanda ya bayyana kadararsa don kashin kansa, a sa’ilin da ya hangi cewa za a bincike shi.
Shugaban hukumar ta EFCC ya yi wadannan kalaman ne cikin wata lacca mai taken, ‘Bukatar yin gyara a sashen Lauyoyi, a farkon fara taron Lauyoyi na kasa.’
An yi laccan ce domin ta dace da babban taron shekara-shekara na kungiyar Lauyoyi ta kasa wanda aka fara ranar Litinin a Abuja.
Magu ya ce, “Lamarin da bakanta rai, ka ga Lauyoyi suna amfani da basirarsu da kwarewar su wajen taimaka wa barayin ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati. Abin zai ba ka mamaki in ka ga babban Lauyan da ya karbi Naira bilyan 1.7 daga barawon dan siyasa ba tare da ya yi gezau ba!
“Wannan dai Lauyan da yake shake da tsabar Naira bilyan 3, 765,414,995.24 a asusun sa, Naira milyan, 7, 051,928.24 kacal ya iya biya a matsayin harajin wadannan kudaden. Ita kuwa Naira milyan, 300 da ya karba daga wancan gwamnan na kudu maso kudancin kasar nan a matsayin ladan tsaya masa a shari’ar zaben sa da ya yi a shekarar 2016, sam ba inda aka nu na ya biya harajin na ta.
“Amma a lokacin da ya tsinkayi EFCC tana shirin gudanar da bincike a kansa, nan da nan sai ya hanzarta fake wa a shirin afuwar gwamnati, (BAIDS), domin ya kare kansa daga tuhuma.
Magu ya ce, wani babban Lauyan kuma ya lababa ne ya san hanyar da ya gujewa biyan harajin da ya kai na bilyoyin Naira, sai ya dan sami wani karamin abu ya biya da sunan wai ya biya haraji.
“Wani kuma babban Lauyan wanda ya hanzarta shelanta kansa a matsayin wanda EFCC ke yi masa bi-ta-da-kulli, ya mallaki tsabar kudi sama da Naira bilyan 5.1, wanda kuma akwai tarin haraji a kansa na sama da Naira bilyan daya a tsakankanin shekarar 2010 da ta 2017. Abin bakin ciki, da kyar ya iya shelanta Naira milyan 8, a matsayin abin da ya samu a shekarar 2014 da ta 2015, ya kuma ce wai Naira milyan 10 ne kacal ya samu a shekarar 2016,” in ji Magu.
Magu ya ce, akwai bukatar Lauyoyi su san tushen inda masu hulda da su suka mallaki dukiyoyin su kafin su karbi kudade daga hannun su.
Ya roki Lauyoyin da su rika fifita Nijeriya a kan duk wani kwadayin kudi da suke da shi.
Advertisement

labarai