Khalid Idris Doya" />

Magunguna Masu Arha Na Iya Maganin Cututtukan Hauka Da Ake Fama Da Su—Rahoto

Pills and capsules in medical vial

Masu bincike daga kwalejin jami’ar London,United Kingdom sun bayyana cewar,sanannun magungunan da ake amfani dasu wajen cututtukan sikari da kuma Zuciya, wadanda kuma suke da arha, za a iya amfani dasu wajen maganin cutar tabin hankali wadda ta munana.

Masu binciken sun kara bayyana cewar abubuwan da suka gano lokacin binciken nasu, sun bayyana cewar yana da matukar amfani, saboda kuwa hakan ya nuna yawan lokutan da marasa lafiya ya dace su je asibiti, har ya zuwa lokacin da za a kai ga basu magani su sha.

Kamar dai yadda gidan watsa labarai na BBC ya bayyana, farkon aikin da su masu binciken suka yi, shine magungunan da ake amfani dasu, wadanda kimiyya, ta kiyasta cewar za su iya taimakawa marasa lafiya wadanda suke da cutar tabin hankali wadda ta tsananta.

Ita tawagar ta tsayar da hankalin tane akan magungunan wadanda suke da nasaba da al’amarin daya shafi anti-cholesterol wadanda ake kira da suna statins, wadanda kuma suna iya kawo sauki musamman wajen matsalolin da suka kunshi tabin hankali, ko kuma taimaka ma jiki ya yi amfani da magungunan da suke maganin tabin hankali.

Magungunan hawan jini wadanda za su iya yin wani abu dangane da sinadarin calcium, wanda kuma hakan zai bayyana ma kwakwalwa cewar ansamu wata haduwa da wata matsalar bipolar da kuma schizophrenia, wanda kuma aka yi sa’a suna daga cikin abubuwan data fi maida hankali dangane da su, har ma da  wadanda suke magani cutar  sikari ta 2  ana kuma kiran su da suna ‘metformin’.

Maimakon a gwada su, sai su masana ilimin kimiyyar suka fara yin bincike saboda su samu wani abinda zasu dogara da shi, wanda kuma suke ganin zai iya taimakawa, saboda kuwa sun duba bayanai na marasa lafiya mutane 142,691, a kasar Sweden, wadanda suke fama da matsalar schizophrenia, bipolar da kuma sauran matsalolin da suka shafi tabin hankali da suke da tsanani.

Sun dai fara lura ko kuma yin bincike akan  lokacin da su masu tabin hankalin, aka duba su , ko kuma kwantar dasu , a asibitin masu tabin hankali, lokacin da suke amfani da maganin da kuma lokacin da basu yi amfani da maganin ba.

Daya daga cikin masu binciken a kwalejin jami’ar London Dokta Joseph Hayes, ya bayyana cewar, binciken ya nuna an samu raguwar kashi 10 zuwa 20, akan abubuwan da ake samu lokacin da muatne suka zo wajen magani.

Sakamakon wanda aka wallafa a cikin mujallar The result, which was published in the journal, JAMA wadda ta mayar da hankalin ta a al’amarin tabin hankali, abin ya nuna cewar an samu raguwar wadanda suke ji ma kansu rauni..

Hayes ya kara jaddada cewar,“ Shi al’amarin yana da matukar burgewa  ganin yadda duk abubuwan suka kasance, amma kuma ai wannan somin tabi ne ma ai.”

Akwai wani binciken wanda akla yi wanda kuma shi mawallafin yana daga cibiya dake lura da al’amuran masu tabin hankali, dake a King’s College London Dokta James MacCabe ya bayyana cewar, “ Su wadannan abubuwan da aka gano wato sakamakon zai yi matukar amfani, wadanda kuma suke nune cewar su kwayoyin zasu taimaka ma wadanda suke da tabin hankali. bayan sunn yi amfani da maganin.

Amma kuma akwai wani abu daya wanda yake damuwar ko su ma masu binciken, shine yadda tafiyar da shi binciken.  Bincike- binciken da aka yi sun kwatanta wani bangare na wadanda basu da lafiyar, wadanda kuma suke shan magani, da kuma wadanda basu shan maganin.. Wannan ya danganta yawan marasa lafiya, a al’amura daban – daban nan rayuwarsu, lokacin da ko dai suna shan maganin ko kuma basu shan shi.

“ Hanyar da aka bi ta binciken da akwai abubuwan da za a karu da su sosai, amma kuma wannan ya nuan sai idan mutane suna zaune lafiya, babu wata hatsaniya.Wannan kuma ya nuna idan mutane suna cikin natsatsen wuri, amma kuma idan aka ga da akwai yiyuwar zuwa asbitin, har ma a kai ga kwantarwa watakila,  ko kuma zasu iya kulawa da kansu su rika shan magani kamar dai yadda,” MacCabe ya kara bayyanawa  daga karshe.

Exit mobile version