Magunguna A Musulunci: Sharrin Aljannu A Kan Hana Samun Miji Ga Mata

07017790084  magungunaamusulunci@gmail.com

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata mun tsaya wurin da na ba da labarin wani bawan Allah da muka yi karatu da shi a gaban Sudais, ya fada min matsalarsa ta abin da yake damunsa, na fara yi masa aiki aljaun wurin suka bayyana mana komai, aka kira wasu aljanun suka tabbatar da cewa lallai asiri aka yi aka ajiye a karkashin gidan, aljanun suka yi tafiyarsu, saboda haka ko an yi Rukiyya ba za su ji ba.

To a yau za mu dora har ya zuwa abinda ya sawwaka, domin har yanzu dai muna cikin duniyar aljanu inda muka karanto suffer Shaidanun aljanu ga mutane. Inda Allah Ta’alah yake cewa ‘’Asshaidanu yu’idukumulfakara wa ya’a mura bil fahsha’i, Wallahu Ya idukum magfiratan minhu wafadhlah, Wallahu wasi’un Alieem.’’

Shaidanun aljanu suna haifar wa da mutane talauci, kuma suna umartarsu da aikata alfahsha. Talauci iri biyu ne, akwai Ma’anawi da hakika wanda duka suna haifarwa.

Ma’anawi shi ne, ga arzikin amma babu wadatar zuci, kamar yadda manzon Allah SAW ya ce; ‘’Laisal Gina an kasuratil ardhi, Walaakinnar gina Ginannafsi.’’ Wato mawadaci ba shi ne mai tarin dukiya ba, sai dai mawadaci shi ne mai wadatar zuciya.’’

Talauci Hakika kuwa shi ne, mutum ya rasa dukiya, shin kudi ne koko kadara ce, wato ya dawo talaka, kamar yadda Manzon Allah ya inganta addu’arsa yana cewa; ‘’Wa’a uzu bika min fitnatil Fakari’’ ‘’wato Allah ina rokonka ka kare ni daga fitinartalauci.’’ Don haka wasu masu kudin da kuke ganinsu, gas u da dukiya mai tarin yawa, amma ba sa hutawa, kullum suna cikin nema ba dare ba rana, kuma ba sa iya taimakawa koda a unguwarsu, kuma koda ma za su yi sai su yi don Riya. To wadannan suna da manyan aljanu a tare da su, wanda suke bukatar su zo mu basu magani.

Haka wasu ma da za ku gani a cikin talauci, ko kuma suna da shi amma sai baya yake yi, z aka samu ko dai aljanu, ko kuma sihiri ne. domin Hadisi ya tabbata cewa ‘’Aballaha an yaj riyal ash yaa a Allah bil’ asbab’’ ‘’Wato Allah Ta’alah baya gudanr da lamari sai da dalilai’’ kuma yana daga cikin Imani riko da sababi, kamar yadda Ibnu Abbas yake fada; ‘’Kamar haka Shaidanun aljanu suka shafi Annabin Allah Ayyuba Alaihissalam, suka cutar da shi cuta matsananiciya.

Inda Allah Ta’alah yake cewa; ‘’Wazkur Abdana Ayyuba Iz nada Rabbahu Anni massaniyasshaidanu binusbin wa azaab.

Wato ‘’Ka ambaci bawanmu Ayyuba lokacin da Shaidanun aljanu suka sa masa ciwo, sai yake addu’a cewa lallai  Shaidan ya shafe ni da ciwo da azaba.’’ Shi ya say a zo a cikin littafin (Lakajul murjan Fi ahkaamul Jan) na Imamu Siyudi da littafin Zuhdu na Imamu Ahmad, da Zuhudu na Abi Hatim, duka daga Ibnu Abbas (RA) yake cewa; ‘’Wata rana Shaidanin aljani ya hau can sama inda yake zama ya yi addu’a, sai ya ce, ya Allah mai gudanar da al’amurana ka bani iko akan Annabinka Ayyuba.’’

Sai Allah Ta’alah ya ce; ‘’ Na amsa maka nab aka dama akan dukiyarsa, amma ban baka dama akan jikinsa. Saboda haka sai ya sakko cikin duniya ya tattara rundunarsa ta Shaidanun aljanu ya ce; ‘’An bani dama akan Annabi Ayyuba, don haka ku je ku yi aiki akansa.’’ Nan da nan sai wasu suka zama wuta wasu suka zama ruwa suka mamaye komai na shi na duniya.

Wasu suka afka wa rakumansa, wasu kuma shanunsa, wasu dabbobinsa kanana, saboda haka sai musiba ta yi bayyana akan dukiyarsa wata akan wata, sai duk aljanun da suka aikata wannan aikin suka canja zuwa suffar mutane suka je wurin Annabi Ayyuba, suka ce da shi; ‘’Shin baka ga yadda Allah ya turo da bala’I dukiyarka ba, alhali kana yi masa biyayya? Sai ya yi bai da su komai ba, daga nan ne komai na shi na dukiya ya kare babu komai sai matarsa da ‘ya’yansa maza 7 mata 7.

To wata rana suna zaune da ‘ya’yansa suna cin abinci, sai wadannan aljanu suka rikida zuwa guguwa mai karfi inda suka ture ginin gidan a kansu, nan take gaba dayan ‘ya’yansa suka mutu. Sai ya rage daga shi sai matarsa, sai wani aljani ya zo a suffar yaro ya ce da shi; ‘’Kai Annabi Ayyuba dubi yadda Allah ya turo iska ta rufto ginin gidanka akan ‘ya’yanka duka sun mutu.

Sai Annabi Ayyuba ya tambaye shi cewa ‘’To kai a wannan lokacin kana ina’’ sai ya ce’’Ina wurin,’’ sai Annabi Ayyuba ya ce; ‘’To ya akai ka tsira?’’ sai aljani ya ce; ‘’Guduwa na yi.’’ Sai Annabi Ayyuba ya ce; ‘’Tafi ka bani wuri, ina neman tsarin Allah daga kai, domin kai Shaidani ne.

Saboda haka Iblis da ya ga bai ci nasara akansa ta wannan hanyar ba, sai bakin cikin ya kama shi har ya kwalla kara da ‘yan sama da kasa sai da suka ji, sannan ya kara komawa sama wurin addu’arsa ya sake rokon Allah ya ce, ‘’Allah ka yi min taimakon da ya fi wannan, domin in ba taimakonka ba zan iya ba.’’ Masu karatu mu hadu a mako mai zuwa idan Allah ya kaimu, wassalamu alaikum warahmatullahi wa barakaatuhu.

 

 

 

Exit mobile version