- KANUMFARI: Wanda yake fama da ciwon kai irin na Mura ko sanyi, Ko Jiri, ya nemi garin Kanumfari cokali biyu ko Uku, ya dafa shi da ruwa. Bayan ya dafu sai a sa ruwan Khal cokali biyu, a sanya Sugar sannan a sha.
In sha Allahu koda majinace ta daskare a cikin Kirjin mutum to za a samu sauki da izinin Allah. - KABEWA: Kabewa idan aka dafa, ka samo ruwanta ka hada ta da sikari ka rika sha. In sha Allahu yana magance yawan ciwon kai.
Kuma namiji wanda yake fama da rauni wajen biyan bukatar iyalinsa, ko kuma mace wacce take fama da matsalar daukewar sha’awa, ko bushewa za su samu sauki.
Haka nan mutumin da zuciyarsa take yawan bugawa da Karfi shima idan yana shan ruwan kabewar zai samu sauki in sha Allah. - HABBATUS SAUDA: Ka samu rabin kofi na ‘ya’yan Habbatus sauda, Kanumfari cokali biyu, Yansun ma rabin kofi. Ahadasu a daka a turmi. Sannan a rika dibar cokali biyu ana dafawa da ruwa kofi daya. Idan ya dahu sai a barshi ya huce, daga nan sai a zuba Zuma, a rika sha.
Masu ciwon kai, masu Olsa (Ulcer) gyambon ciki, masu Hawan Jini, masu ciwon kirji, masu tsakuwar Koda, idan suna shan wannan za su samu lafiya da izinin Allah. Za a rika sha safe da yamma ne. - LEMON ZAKI: A samu bawon Lemu a yanyanka shi kamar cikin Kofi guda, a dafa shi da ruwa kofi biyu. Idan ya tafasa sai a sauke. A tace da rariya sai kuma a sa zuma a rika shan sa safe da yamma.
Masu Ccwon Kai da masu fama da kumburin ciki ko rashin narkewar abinci za su samu lafiya. - NA’A-NA’A: A samu ganyen Na’a-Na’a, ganyen Raihan, a dafa su tare da Kanumfari a rika sa zuma, ana shan ruwan da ‘duminsa, Sannan a rika goga ganyen akan goshin maras lafiyan.
Wannan maganin Ciwon kai ne babu karya, kuma yana magance cutar kumburin jiki, yana magance ciwon sanyi na mata, da kuma magance ciwon daji (Cancer) cikin ikon Allah. - SANA-MAKKIY: Cokali uku na sanamiki, Cokali uku na garin Habbatus Sauda, Cokali biyu na chitta. Ahadasu adafa da ruwa kofi biyu Sannan asanya Sugar arika sha safe da yamma. Sannan arika shafa MAN CHITTA (Ginger Oil) akan goshin marar lafiyan.
In sha Allahu kai zai dena ciwo. Idan kuma Jiri ne ko Hajijiya shi ma za a samu lafiya in sha Allah. - MAN HABBATUS SAUDA: Arika shafawa akan marar lafiyan in sha Allahu kan zai dena ciwo. Amma za a rika maimaitawa safe da rana da yamma.
- MAN RAIHAN: A hada man raihan da man Hasa-lebban, tare da turaren Wardi a hada wuri daya a rika shafe jikin marar lafiyan baki daya. Bayan an karanta Fatiha 7, Ayatul kursiyyi 7, Suratul Feel 11,Kul Huwallahu 11, Falaki da Naasi 11 a tofa cikin wannan hadin.
In sha Allahu wannan maganin ciwon kai ne sosai. musamman irin wanda Shaitanun Aljanu suke haddasawa. Kuma yana magance Ciwon jiki Ko shanyewar gabobii irin wanda Aljanu ke sanyawa. - Furen Albabunaj: Ana tafasawa asha cokali biyu, ana shan sa safe da yamma kamar Shayi, in sha Allahu za a ga abin mamaki wajen samun waraka daga ciwon Kai, Ciwon Koda, Rashin barci, faDuwar gaba, Makalewar fitsari, da dai sauransu.
Kanunfari na daya daga cikin abubuwan da muke amfani da su a matsayin sinadaren kamshi a cikin abinci ko abun sha. Ko kun san cewa alfanun sa ya wuce gaban haka?
Kanumfari na dauke da dumbin sinadaran kara lafiya da magance cututtuka da dama domin yana maganin cututukkan da bama iya ganin su kai tsaye ba tare da an saka madubin Likita ba (micro sort). Ga yadda za a yi amfani da kanumfari wajen neman lafiya:
(1) Ciwon Kai
- A) Yana maganin ciwon Kai. A shafa man kanimfari a goshi, Yana taimakawa wajen ciwon Kai da ke faruwa sanadiyar mura.
- B) Idan kuma ciwon kan ba na cutar mura ba ne, za a iya samun Kanumfari guda biyar a sa a cikin ruwa kofi guda, a dora shi a wuta su tafasa sosai sai a sa sikari kamar rabin cokali a ciki, idan ya dan huce sai a sha a yi haka sau biyu a yini, In sha Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa ba ya yin magani ne.
(2) CIWON HAKORI: Yana maganin ciwon hakori. Za ka iya amfani da man- kanimfari (clobe oil) ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin (dakakke), a jika shi kadan da ruwa a lika wajen hakori mai ciwo. Idan mai (clobe oil) kake amfani da shi sai a samu auduga a zuba man kadan a lika wajen hakori mai ciwo (ka danne da hakora).
(4) Maganin Amai
(A) Domin tsayawar amai ga masu ciki, a daka kanumfari biyu a sa babban cokali daya na zuma a sha, yana maganin amai ga mace mai ciki.
(B) Don magance amai ba ga wadda take da juna biyu ba, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sikari cokali daya a sha.
(5) TYPHOID: A samu ruwa lita biyu ta ruwa sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan ya koma sauran lita daya sai a sauke idan ruwan ya huce sai a rika sha Wannan yana maganin typhoid.
(6) Ciwon Kunne: A hada man kanunfari da man Ridi a diga a kunne mai , duk lokacin da za a kwanta bacci wannan yana maganin ciwon kunne.
(7) Maganin Mura: Ga masuyin mura A tafasa shi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.
(8) Maganain Makero/Kyanda: Ana goga man kanumfari a wurin da matsalar take wannan yana maganin makero.