Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home KIWON LAFIYA

Magungunan Gargajiya: Mu Na Magance Cutar Ƙarin Mahaifa Da Kansar Nono (II) —Dakta Nasiru Sani

by Tayo Adelaja
October 2, 2017
in KIWON LAFIYA
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ci gaba daga bugu ta 012

 

Waɗanne cututtuka ne Ke da wuyar magani a asibitocin zamani ku Kuma ku ke warkar da su cikin sauƙi?

Godiya ta tabbata ga Allah, na ji daɗin wannan tambaya ƙwarai da gaske. To suna da yawa amma dai ga misali kaɗan daga ciki kuma in dai likitan zamani ya san abin da yake kuma zai yi adalci ba mun ce ba su iya ba ne kuma ba muna raina musu ba ne a’a muna yaba musu a kan ƙoƙarinsu duk da ba kasafai wasu suka yarda da mu ba ko kuma suke yaba mana ba amma wasu sun yarda da mu a cikinsu kuma suna yaba mana.

Misali na biyu zan ba ka, na je wata mu’amalata zan ga wani a ɗaya daga cikin manyan asibitocin da ake taƙama da su a nan Kano sai na ji wata magana kamar daga sama wata mace na cewa ita matsalar da take fama da ita ita ce ta ɗaukewar ni’ima. Ta ce, ta yi magani ta ga manyan likitoci a kan wannan matsalar amma abin ya ci tura! Sai na ji wata ƙwarariyar likita tana cewa gaskiya sai dai ki nemi na Hausa, wato maganin gargajiyya ƙwarariyar likitan zamani ce ta ke gaya mata haka, to tunda na ji sai na ce to shi ke nan ni kuma zan taimaka mata ta turo mai gidanta ko wani nata ya zo ya same ni. Abu kamar wasa ta zo maganin da na ba da asha da kunu ne, na ce tasha asha na farkon rana ɗaya ta ce ta ga alamun nasara mijinta ya bugo min waya ya ce matarsa ta kwana cikin farin ciki amma ta yi shekara da shekaru tana kai da komowa a tsakanin manyan likitoci amma Allah bai kawo warakar ba, sai ta dalilinmu kuma wasu cututtukan za ka ga a asibiti ko sun warke za ka ga sun dawo bayan wata uku ko ’yan watanni ammma mu in muka bayar asha a shafa sai ka ga Allah ya warkar da cutar gaba ɗaya ta sanadinmu kuma mu muna da ilimin cewa duk magani da ka sha kwana uku ba ka ga alamar sauƙi ba to ba zai yi ba a sake wani.

Ganin irin wannan basira da baiwa da Allah ya yi muku ko kuna zama da likitocin zamani a ƙara wa juna sani domin amfani al’umma?  

To da muna zama a tattauna ƙarƙashin manyan masana lafiya Daktoci da Farfesoshi a wannan zama a ƙarƙashin wani Kwamiti to kasancewata ni mutum ne mai tafiye- tafiye ƙasashe daban- daban a kan wannan harka, to da na yi wata tafiya sai wannan Kwamiti ya samu targaɗo to sai aka daina amma yanzu muna ƙoƙarin kafa shi ya zama ya ɗore domin saboda kyaukkyawar dangantaka har ma daga jami’a ana turo mana ɗalibai masu alaƙa da wannan fannin sanin makamar aiki a gunmu kuma ko bana ma an turo mana aƙalla ɗalibai 17 duk da dama suna turowa amma dai bana ne sai an yi a rubuce kamar yadda ake tura su wasu gurare.

Na ji ka ce kana yawan tafiye- tafiye ƙasashen duniya kan wannan harka ƙasashe nawa ka je?

Na je ƙasashe da yawa misali naje ƙasar nigar ita wannan kamar gida ne Kamaru, TurKiya, Spain, Ghana, Misira, Algeria, Indiya, China, Iran, Saudiya da dai sauransu wasu muna zuwa neman ilimi ne a kan wannan fanni namu na gargajiya wasu su ne suke gayyatarmu mu je mu yi masanyar ilimi, wasu kuma muna zuwa neman magunguna ne kamar Aljeriya ita na je na yi noma wani magani ne kamar Saudiya ita gida ne wasu cibiyoyin lafiya ne ko hukumomi ne suke gayyatarmu, kamar Iran wata cibiyar lafiya ta gayyace ni mun ƙaru juna sani a kan magugun nan gargajiyya.

To a ƙarshe wane saƙo kake da shi ga gwamnati musamman hukumomin kula da lafiya na ƙasa da na jahohi?

To saƙona shi ne mu masu maganin gargajiyya waɗanda muke buncike sosai a littatafai na Musulunci da sauran hanyoyi na sani ilimin magani kuma magani an jarraba an ga ya yi ba matsala in wani bai san haka ba wasu sun sani, to tunda haka ne kuwa muna da gudunmawa mai yawa da za mu bayar in an haɗa kai da mu 100 bisa 100. Kuma muna mamakin yadda hukumomin lafiya suke kashe kuɗi mai yawa a kan harakar lafiya wanda idan aka haɗa kai da mu za a samu biyan buƙata kuma a rage kashe kuɗi kamar yadda wasu ƙasashe da muka gani a duniya sun san haka kuma sun yarda da haka kuma sun yi nisa a kan aiki da maganin gargajiyya saƙona shi ne gwamnati ta ja mu a Jiki, akwai gudunmawar da za mu bayar mai yawa idan an yi haka. su kuma masu maganin gargajiyya da likitoci da sauran al’umma su ji tsoran Allah.

SendShareTweetShare
Previous Post

Wayoyin Balackberry Na Gab Da Shiga Kwandon Tarihi

Next Post

Agogon Phillepe Patek: Agogon Da Ya Fi Tsada A Duniya

RelatedPosts

Cutar Kyanjamau Ko Sida

Cutar Kyanjamau Ko Sida

by Sulaiman Ibrahim
3 days ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Su kwayoyin cutar sida (da Turanci...

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

Me Ke Kawo Karkacewar Baki Kwatsam?

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Mustapha Wakili da Muhammad Zahraddin Shanyewar barin fuska larura...

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Ruwa Da Amfaninsa A Jikin Dan Adam

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Amfanin ruwa guda tara a jikin dan Adam idan ya...

Next Post

Agogon Phillepe Patek: Agogon Da Ya Fi Tsada A Duniya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version