Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mahaddata 123 Ne Suka Gwabza A Minna

by
4 years ago
in LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

An kira ga ‘yan Nijeriya da su tantance mutane masu gaskiya a lokacin babban zabe mai zuwa, domin rashin Shugabanci na gari ya assasa halin da ta ke ciki yanzu, kafin zuwan wannan gwamnatin kasar ta shiga halin a ya zamo al’umma sun debe tsammanin zaman kasar wannan waje daya. Ya zama wajibi ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da juna, domin zaman lafiyar nan shine ginshikin cigaban kasa. Shugaban kungiyar Izalatul Bid’a Wa’ikamatus Sunna ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ne ya yi kiran a lokacin bukin kammala gasar karatun Al-kur’ani mai girma na kasa karo na ashirin da biyu wanda ya gudana a dakin taro na U.K Bello da ke minna.

Dan haka ya kamata ‘yan Nijeriya su goyi bayan gaskiya, domin gaskiyar nan kadai ce za ta jagoranci kasar nan ga hawa tudun natsira.

Wajibi ne idan lokacin zabe yazo mu tabbatar mun zabi shugaba tsayayye da zai rike kasar nan da amana, don haka jama’a kar su yarda da ‘yan siyasar hoto da farfaganda, lallai ne su zabi mutane masu amana, domin ha kan ne zai zamo ginshikin zaman lafiya a kasar nan.

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

Tunda farko a bayaninsa, gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya cefitintinu ne da ke taso wa a kasar nan musamman jahohin Fulato da wasu jahohin kasar nan ya samo asali ne daga wasu gurbatattun mutane kuma gwamnati na kokarin ganin ta kawo karshen wannan lamari, dan haka dole ‘yan Nijeriya mu zauna tare ba tare da nuna bambamcin addini ko yare ba, addini ko jinsi ba, saboda haka ya zama wajibi mu cire bambamce bambamce a tsa kanin dan kasar ta cigaba. Gwamnan dai ya alkarwanta cewar duk gwarazan da suka samu nasara a wannan musabakar da ake gudanarwa koda ya dauka a kan kujerar ta gwamna. Gwamna ya jawo hankalin ‘yan siyasa a kan zaman lafiya, ya cea matsayin ka na dan kasa kana da damar tsayawa takarar siyasa, amma idan ka fadi sai ka hakura sa ke jarabawa a gaba, yin anfani da ‘yan bangar siyasa a lokacin siyasa ba alheri ba ne, domin ha kan ba abinda haddasawa illa bata tarbiyar matasa.

Gwamnan dai ya bada naira dubu dari biyar ga wanda ya zama gwarzon shekara, ya yin da dubu dari uku zasu tafi ga wanda yazo na biyu, wanda ya zamo na uku zai samu naira dubu dari. Gwamnan dai ya cewannan kudin zai cigaba da bada su kowace shekara koda bayan saukarsa a kan mulki ne, ya cehaka zai karawa matasa wajen dagewa wajen inganta tarbiyarsu ta hanyar addini.

Abubakar Sadik Yunus daga jihar Adamawa ne yazo na uku, ya yin da Nasir Ridwan daga jihar Bauchi ya zama na biyu, Umar Abdullahi Shu’aya’u daga jihar Jigawa shi ne gwarzon shekara a wannan masabakar ta bana a bangaren kungiyar Izala wadda Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagorantar majalisar malamai ta kasa.

Taron dai ya samu halartar gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da mataimakinsa, tsohon shugaban ma’aikatan jiha, Kadi Kuta, shugabannin majalisar dokokin Neja da Kebbi, sai mataimakin shugaban majalisar malamai ta kasa da mataikansa, Sheikh Yusuf Sambo Rigacikun da Sheikh Alhassan Sa’idu Jingir. Jahohi goma sha tara, da jamhuriyar Nijar da kasar Benin ne suka halarci taron musabakar da ‘yan takara 123, taron dai an gudanar da shi ne tsawon sati daya da inda mai maraba Etsu Nupe ya wakilci mai maraba Sarkin musulmi.

ADVERTISEMENT

Da yake karin haske, daraktan kula da harkokin addini, Dakta Umar Faruk Abdullahi, ya cewannan masabakar gwamnatin jiha ce ta dauki nauyinsa, ya cegwamnatin tayi haka ne dan karawa mahaddata Al-kur’ani mai girma himma, domin da irin wannan dubarar ne za a iya canja tunanin matasa a irin halin da su ke ciki yanzu.

Ya ceyanzu haka gwamnati za ta bullo da bangaren haddar Al-kur’ani a makarantun Islamiyyu da ke jihar, domin ba wani abinda za ka baiwa yara masu taso wa da ya wuce shagaltar da su daga wasu dabi’un da basu dace da al’adun mu da addinin mu ba. Ya zama wajibi gare mu assasa Al-kur’ani a cikin zukatan yara masu taso wa a dukkanin bangarorin jihar ba tare da nuna bangare akida ba illa musulunci zalla.

Dakta Faruk ya jawo hankalin Iyaye da su sauke nauyin da ke kansu na tarbiyatar ‘yayan su wanda amana ce a gare su, ta hanyar assasa Al-kur’ani a cikin zukatansu.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Mahaddata 123 Ne Suka Gwabza A Minna

Next Post

Ba Ni Da Muradin Neman Kujerar Sanata A 2019 –Makarfi

Labarai Masu Nasaba

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

Mai Yuwa A Gaza Kawo Karshen Yaki Da Yunwa A Nijeriya Har Zuwa 2025 —Mata Manoma

by Abubakar Abba
6 hours ago
0

...

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

Sojoji Sun Kashe 2 Tare Da Tarwatsa Sansanin Bayar Da Horo Na IPOB A Jihar Imo

by Abubakar Abba
7 hours ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

Batanci: CAN Ta Janye Gabatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Kisan Deborah

by Leadership Hausa
10 hours ago
0

...

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

‘Yan Bindiga Sun Fille Kan Wani Dan Majalisa A Jihar Anambra

by Abubakar Abba
11 hours ago
0

...

Next Post
Ba Ni Da Muradin Neman Kujerar Sanata A 2019 –Makarfi

Ba Ni Da Muradin Neman Kujerar Sanata A 2019 –Makarfi

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: