Connect with us

RAHOTANNI

Mahaifin Marubuciya Sadiya Rimi Ya Kwanta Dama

Published

on

Alhaji Musa Muhammad Inusa, wanda aka fi sani da ‘Musa Rimi Mai-Atamfa’ wasu kuma na kiran sa da ‘Musa Fari’ shi ne mahaifin fitacciyar marubuciyar  nan ta Adabin kasuwar Kano Hajiya Sadiya Musa Rimi. Alhaji Musa Rimi Mai-Atamfa ya rasu ne a ranar Alhamis da ta gabata da misalin karfe 12:20 na dare. A gidansa dake unguwar Hausawa Kano. Ya rasu ne bayan ya yi fama da ciwon ciki na kwanaki Shidda.

Marigayi Alhaji Musa Rimi, ya rasu yana da shekaru Saba’in Da Biyar (75) a duniya. Ya rasu ya bar mace Daya (1) da ‘ya’ya Goma (10) da kuma jikoki Talatin (30). Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Yakubu Musa Rimi da kuma Sadiya Musa Rimi, wacce fitacciyar marubuciya ce da sunanta ya karade kasar Hausa. Hajiya Sadiya Musa Rimi ita ce mataimakiyar shugaba ta kungiyar marubuta ta TSINTSIYA WRITERS ASSOCIATION. Ta rubuta littattafai da dama. Mafi shahara a cikinsu su ne Garkuwa, Maza Gumbar Dutse da kuma In Da Rai…

Allah ya ji kan sa ya masa Rahma ya sa jannatil Firdausi ce makomarsa, ya karawa iyalinsa hakurin rashin sa,  in tamu ta zo ya ba mu ikon cikawa da imani Ameen.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: