Connect with us

LABARAI

Mahaifiyar Leah Sharibu Ta Maka Minista Da Babban Sufeto A Kotu

Published

on

Mahaifiyar yarinyar nan, Leah Sharibu, da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka sace daga makarantar Sakandare ta Dapchi, wacce kuma suke rike da ita a hannun su har yanzun, Rebecca Sharibu, ta maka shugaban ‘yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, da babban Lauyan gwamnati, Abubakar Malami, a kotu inda take neman su biya ta diyyar Naira milyan 500, a bisa abin da ta kira da, yin sakaci da aikin na su, wajen ‘yanto mata diyarta daga hannun ‘yan ta’addan.

Ta nemi kotun da ta tilasta su, su biya ta Naira milyan 500 ne kasantuwan irin zaman kaskanci da cin mutunci gami da wahalar da diyar na ta take fuskanta tun daga lokacin da ‘yan ta’addan suka sace ta a watan Fabrairu 2018.

A jiya, manema labarai sun shaidi ma idonsu kwafin karar wacce aka shigar a ranar 19 ga watan Satumba 2018, mai lamba kamar haka, FCH/L/cs/1528/18, a babbar kotun tarayya da ke Legas.

Bukatun da mai shigar da karar ta nema daga kotun sun hada da, Kotun ta tilasta wa wadanda ake karan da su karbo mata diyarta daga hannun wadanda suka sace ta ba tare da wani sharadi ko bata lokaci ba, kotun ta tilasta wadanda ake karan su biya ta Naira milyan 500, kasantuwan irin zaman kaskanci da cin mutunci gami da wahalar da diyar na ta take fuskanta tun daga lokacin da ‘yan ta’addan suka sace ta a watan Fabrairu 2018.

Takardar shigar da karan ta kara da cewa, “Matukar wadanda ake karan ba su amsa kiran kotun ba su da kansu ko kuma ta hanyar Lauyoyin su a cikin lokacin da doka ta kayyade masu na su amsa kiran na kotu, kotun ta zartar da hukunci kai tsaye a kansu kan dukkanin abin da ake nema a wajen na su.

A cikin takardar tabbacin nu na goyon baya a kan shigar da karan, daya daga cikin masu hannu wajen shigar da karan, kuma babban daraktan wata kungiyar sa kai ta kasar Amurka, mai suna, ‘Lift-Up-Now Incorporation,’ Dakta Adeniyi Ojutiku, cewa ya yi: “Ni Dakta Adeniyi Ojutiku, dan Nijeriya ne, wanda ke zaune a gida mai lamba, 1316 kan titin, Shining Water Lane Raleigh, NC 27614, na kasar Amurka, ina mai rantsuwa kan cewa: ni ne babban daraktan kungiyar sa kai ta, ‘Lift-Up-Now Incorporation,’ a matsayina na aboki na uku, na gamsu da duk abin da wanda ya shigar da karan nan yake nema daga wadanda yake karan kamar yadda aka zayyana a cikin takardar ta shigar da kara.”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: