Mahaifiyar Marubuci Hashim Abdallah Ta Abdallah Ta Kwanta Dama

Marubuci

Hasheem Abdallah fitaccen marubuci ne sananne a duniyar rubutu da marubuta, ya wallafa littattafai da dama da ake cin kasuwarsu a kasuwar adabin Kano, da ma wadanda ake cin kasuwarsu a yanar gizo. Littafinsa na baya-bayan nan da ya zama gagarabadau a cikin littattafansa shi ne ‘Ilimin Rubutun Labari Cikin Adabi Turbar Addini Da Al’ada’.

Mahaifiyar ta marubuci Hasheem Abdallah wato marigayiya Hajiya Halima ta rasu ne sanadiyyar ciwon ciki na rana daya jim kadan da kai ta a sibiti, a ranar Juma’a 10 ga watan Ramadhan, 1442. Wanda ya yi daidai da 23, April, 2021. Marigayiya Hajiya Halima ta rasu tana da shekaru 83 a duniya. Ta rasu ta bar ‘ya’ya 9 da jikoki 63. Daga cikin ‘ya’yan nata akwai Akwai: Aliyu Abdullahi, Shugaban ma’aikatar matasa, wasanni da al’adu ta kasa, Yankin Arewa-Maso-Yamma. Da Hashim Abdallah, lecturer II Binyaminu Usman Polytechnic Hadejia, JIGAWA,

Allah Ya ji kan ta da gafara, Ya haska makwancinta, Ya sa jannatul firdausi ce makomarta, idan tamu ta zo Ya sa mu cika da imani Ameen.

 

Exit mobile version