Nasir S Gwangwazo" />

Mahaifiyar Sarkin Hadeja, Mai Babban Daki Hadiza, Ta Kwanta Dama

Mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Hadeja, Alhaji Adamu Abubakar Maje, wato Mai Babban daki Hajiya Hadiza Abdulkadir, ta rasu tana da shekara 80 a duniya.

Marigayiya Hadiza ta koma ga Ubangiji ne a daren ranar Asabar, kamar yadda Masaraiutar Hadejan ta sanar.
A yayin da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin karamar Hukumar Hadeja, Muhammad Talaki, ya ce, Mai Babban dakin ta rasu ne bayan fama da jinya.
Ya kara da cewa, Mai Babban daki ta rasu ta bar ’ya’ya tara, ciki har da Mai Martaba Sarkin Hadejan, da kuma jikoki da dama.
Tuni dai aka binne ta daidai da tanadin addinin Islama a washegari Lahadi (wato jiya kenan), 14 ga Fabrariru, 2021, kamar yadda kakakin ya tabbatar a cikin sanarwar.
Cikin wadanda suka halarci jana’izar akwai Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, Mataimakinsa Umar Namadi, sarakunan jihar ta Jigawa; Sarkin Gumel da Sarkin Dutse, da kuma Sarkin Machina daga Jihar Yobe da Sarkin Katagun daga Bauchi, wadanda suke makotaka da Masarautar ta Hadeja, tare da sauran jiga-jigan mutane da kuma dimbin al’umma.

Exit mobile version