CRI Hausa" />

Mahalartan Taron Masanan Sin Da Afirka: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Amfani Daukacin Bil Adama

An kira taron masanan kasar Sin da kasashen Afirka karo na tara ta kafar bidiyo da kuma gaba da gaba tsakanin ranakun 5 zuwa 6, inda mahalartan taron suka bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ya taka babbar rawa wajen ingiza habakar tattalin arzikin duniya, haka kuma ya amfani daukacin bil Adama, kuma a nan gaba, ya dace sassan biyu su ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da ajandar AU ta nan da shekarar 2063, da kuma tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka.

Tsohon shugaban Mozambique Alberto Chissano ya bayyana cewa, dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da shawarar ziri daya da hanya daya, sun samar da dabarun da suka dace ga hadin gwiwar sassan biyu, wadanda za su ciyar da amincin gargajiya dake tsakaninsu gaba yadda ya kamata. Ya kara da cewa, yana ganin sassan biyu suna da muradun raya kasa iri guda daya, a don haka hadin gwiwa a tsakaninsu zai kyautata tsarin huldar kasa da kasa, tare kuma da samar da wani dandali mai adalci ga daukacin kasashen da suke sa ran ci gaba da samun wadata.
Babban jami’in kungiyar nazarin kimiyyar al’adu ta kasar Afirka ta kudu Crain Soudien shi ma ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta soke ko rage basusukan da take bin kasashen Afirka, lamarin da ya sassauta matsin da kasashen ke fuskanta yayin da suke kokarin kandagarkin annobar cutar COVID-19, yana mai cewa, kasar Sin tana son kiyaye moriyar kasashen Afirka, kuma tana kokarin biyan bukatunsu, inda ya ce, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ya kasance abin koyi ga kasashe masu tasowa yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu.(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

Exit mobile version