Mahara Sun Kashe Mutane 30, Sun Tarwarsa Garuruwa Da Dama A Zamfara

Direbobi

Daga Hussaini Yero,

A yanzu haka Mahara na cigaba da kashe mutane a kauyukan Jihar Zamfara ,sun kashe mutane 30 a kauyukan,Dutsen Gari da Tali gundumar Kanoma cikin Karamar hukumar Maru.

Daya daga cikin wadanda aka kashe ma ‘yan uwa uku a garin Tali ya bayyana wa manema labaru cewa,”Wadannan maharan sun dade sunayi masu dauki dai dai,kafin suzo su tarwarsa garin ,dan yanzu haka muna ciki garin Kanoma da mu da wadanda suka saura da rayukan su.inji daya daga cikin ‘yan gudun hijira daga garin Tali.

“Kande Bawa itama ta bayyana wa manema Labarai cewa,”Yan ‘yanta  bakwai amma da biyu ta tsira da su batasan Inda sauran su ke ba.kuma a gabana naga gawarwaki 20 , wadanda akai wa yankan rago.

Yanzu haka dai a Garin Dutsen Gari,alumar garin sun tarwatse sabo da yadda maharan ke cinkaren su babu babaka.dan a watanin baya maharan sun kwashe mutane sama da dari a Masalacin Juma’a ana sallar Juma’a saida akai bada milyoyin kudi wajan amso su.

A tattaunawar Kwamishina tsaro ,Hon Garba Dauran ,ya bayyana cewe,’Sun samu labari abunda kefaruwa a kauyukan kuma gwamnati da jami’an tsaro na iyaka kokarin su wajan magance matsalar.

Wakilin mu ya nemi jin ta bakin jami’in hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sanda na jiahr,SP , Muhammed Shehu Amma abun ya ci tura wayar sa taki samu.

 

Exit mobile version