Mahara Sun Kashe Mutum 13 A Neja, Da Dama Suna Jinyar Harbin Bindiga, Mutanen Gari Sun Yi Shahada Wajen Turjiya Ga ‘Yan Bindigan

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

Tun bayan da mahara masu dauke da bindiga suka kaddamar da hare-harensu a yankin masarautar Kontagora da ke jihar Neja, zuwa yanzu kauyuka da dama sun tarwatse, sai dai kuma an samu wadanda suka yi shahada tare da afka wa maharani da zarar sun kawo hari.

Bayan harin da ya kai ga salwantar rayuwar sardaunan Kontagora, Bashir Sa’idu Namaska, maharan ba su tsaya ba, sun sake kai hari ranar Juma’a a karamar hukumar Rijau inda ya kai ga bai wa jami’an tsaro nasarar kashe maharan da dama a ranar Juma’ar da ta gabata.

Bayan harin Rijau, maharan sun yi yunkurin sake kai wani harin garin Ibeto ta karamar hukumar Magama, wanda aka yi dauki ba dadi tsakanin maharan da mutanen Ibeto da ya kai jikkita dukkanin bangarora, tare da kai wadanda suka ji raunuka babban asibitin gwamnati da ke Kontagora.

Bayan harin Ibeto maharan sun sake kai wani hari a Mangwaro da ke karamar hukumar Mariga, inda suka samu turjuyar mutanen gari da ya kai ga kashe mutanen goma sha uku tare da jikkita wasu da dama, inda rahotanni suka tabbatar da cewar sakamakon turjiyar mutanen Mangwaro ya kai ga kassara maharan da dama, wanda ya tilasta masu janyewa.

Rahotanni sun tabbatar da cewar mutanen Mangwaro sun zabi yin shahada maimakon hijira tare da tabbatar da kare kasar su, wanda ya baiwa mata da maza kwarin guiwar tsayin daka dan ganin maharan ba su samu nasara akan su ba.

Wani ganau, ya shaida ma wakilin mu a wayar tafi da gidan ka cewar lallai mutanen Mangwaro ba su tafi ko ina ba, sun fafata da maharan da suke da tabbacin yin illa ga maharan wanda ya janyo mutuwar mutane sha uku ‘yan asalin Mangwaron tare da raunata wasu da dama da yanzu haka ke kwance a asibiti dan karban magani.

Ganau din ya ce lallai akwai kauyuka da ke makota da garin Mangwaron da suka watse dan gudun hijira saboda tsoron kar maharan su far masu, musamman ganin irin illar da aka yi masu a Mangwaro.

Hon. Abdulmalik Sarkin Daji, tsohon shugaban karamar hukumar Mariga kuma kwamishina a ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Neja, ya ziyarci asibitin dan gane wa idanunsa wadanda suka samu raunukan. A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai ya ce jama’a su kara hakuri kuma su cigaba da yin addu’o’in ganin Allah ya kawo karshen wannan bala’in na maharan.

” Maganar gaskiya gwamnati ta tsaya kai da fata domin ganin an kawo karshen wannan lamari, yace gwamnati da jami’an tsaro suna bakin kokarin su amma akwai bukatar jama’a su kara bude idanuwansu da kunnen su dan gano masu tseguntawa maharan labarai, domin sun fi maharan illa dan daukar matakin gaggawa akan su”, inji kwamishinan.

Hare -haren na kara kazanta ne a daidai lokacin da ruwan sama ke sauka jama’a na kokarin mayar da hankalin su a kan aikin gona a shiyyar masarautar Kontagora da mafi yawan tattalin arzikin yankin ya karkata ne akan noma da kiwo, maharan na aukawa ne da miyagun makamai suna harbin kan mai uwa da wabi tare da yin garkuwa da jama’a da kwashe dabbobi.

Gwamnatin jihar dai tana jinjina wa jami’an tsaro a kan kokarin da suke yi, sai dai a kullum tana kira ga gwamnatin tarayya wajen kara karfafa guiwar jami’an tsaron da kayan aiki ganin mafi yawan lokutta maharan kan zo da adadin da yafi yawan jami’an tsaron da miyagun kayan fada.

Exit mobile version