Mahara Sun Kashe Shanu 73 A Nasarawa

A shekaran jiya ne Fulani mazauna dajin Madaga dake kauyen Kadarko a yankin raya kasa ta Giza cikin karamar hukumar Keana a Jihar Nasarawa  Suka wayi gari cikin tashin hankali a lokacin da wasu mahara suka kai masu hari bayan idar da sallar asuba.

Da yake zantawa da manema labarai Kwamishinan Yan Sandan Jihar Nasarawa Bello Ahmad ya ce maharar sun kawo hari ne da Asuba inda suka ci gaba da bude wuta kan Shanun dake kwance a garke.

Ya ce, harin yayi sanadiyar halaka shanu 73 yayin da guda 18 suka tsira da munanan raunuka. Ya kara da cewa Mutum shida sun bace ba a gansu ba, amma daga basani Rundunar ’Yan Sanda ta gano mutum hudu saura mutum biyu har yanzu ba a san inda suke ba.

Kwamishinan ‘yan Sandan ya ce, Rundunar yan Sandan za ta ci gaba da bincike har sai ta gano inda sauran Mutum biyu Fulanin suke.

Dajin Madaga dake kan iyakan Jihar Nasarawa da Binuwai ya watse babu kowa  cikinsa saboda da kowa na gudun bai san me zai biyo baya ba.

Wakilinmu, ya isa dajin Madaga tare da tawagar Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Nasarawa Bello Ahmad domin ganewa idanunsu abin da ya faru a yammacin lahadin.

Kwamishinan Yan Sandan yayi kira ga al’umman Jihar Nasarawa da su kwantar da hankalinsu wajen taya Rundunar Yan Sandan Jihar Nasarawa ci gaba da aiki ba dare ba rana, har sai ta dakushe masu kokarin haddasa rigima a wanan Jihar.

Ya ce, maharan sun yi amfani ne da bindigogi wajen kai harin, ya kara da cewa ba a da tantace maharan ba Amma da Ikon Allah za su shiga hannu.

 

Exit mobile version