Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home RAHOTANNI

Mahara Sun Kashe Shugaban ’Yan Bangan Jihar Kaduna

by Tayo Adelaja
September 20, 2017
in RAHOTANNI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

A daren ranar Lahadi17 ga watan Satumbar 2017 ne wasu gungun mutane dauke da muggan makamai suka afka gidan shugaban ‘yan bangar jihar Kaduna, Malam Mustafa da ke anguwar Katsinawa a gundumar Shika da ke Jihar Kaduna.

Daga Idris Umar, Zariya

Wakilin LEADERSHIP A Yau ya samu lekawa garin da wannan lamarin ya auku kuma ya tattauna da wanda lamarin ya rutsa da su har sun masa cikakken bayani.

Salmanu Mustafa wanda yanzu haka yana jinya ne a gidansu sakamakon azabar da ya sha a wajen maharan, amma duk da haka ga abin da ya gane wa idonunsa ya ce: “A daren Asabar ne da misalin karfe 2 sai muka ji maganar wasu mutane su kimamin 20 a bayan gidanmu, jim kadan sai muka ji kuma sun fara dukan kofofin gidanmu hakan ya sa duk muka tashi ni da kannina, mata guda 3 Hasana da Husaina da Najimatu da iyaye na,bayan haka sai kowa hankalin sa ya tashi. Daga kalaman da suke fadi sai muka gane cewa ‘yan fashi ne kawai yau mun shiga uku sai muka fara kiran mutane ta waya. To ashe suna jin mu ta bayan gida duk maganar da muke yi shi ya sa suna shigowa sai suka kwace duk wayoyinmu suka cire layukan amma dubara ta zo min na boye wasu a wani sako har da na Babana.

“Bayan duk sun gama razana mu sai suka fasa kofa suka shigo cikin gida suka fasa kofofin na dakunanmu suna cewa, ina Babanku? Ina kuka boye shi? Ina gwal? Ina kudi? Nan take sukai ta dukan mu nan take suka harbi Babanmu ya fadi kasa warwas, da suka ga ya fadi, sai suka fito da mu kan titi suka kwantar da mu suka ce in har ba mu ba su kudi ba sai sun kasha mu. Ga shi mu kuma ba mu da kudin da suke tunani.

“Bayan sun mayar da mu cikin gida, can sai ga motar ‘yan sanda ta shigo unguwar a guje sai suka hau ta da harbi sai motar ta wuce a guje. Hakan ya sa suka kara matsa mana har suna cewa, tunda kuka kira mana Police to wallahi kun shiga uku. Daga nan ne sai suka ce wa Mahaifiyata tunda kun hana mu kudi to wallahi za mu tafi da ke, don har suna tambayar ta cewa ko ki zabi daya da mu tafi da yaranki mata da mu tafi da ke wanne kika fi so? Sai Mahaifiyata ta ce don Allah ku tafi da ni, amma ku bar min yarana. Sai suka ce to mun ki da yaranki za mu tafi.

“Da suka gama mana wulakanci ne sai suka tafi da kannena su uku Hasana da Husaina da yata babba Najimatu can bayan kusan awa daya sai ga Husaina ta dawo da yake ita ce karamar cikinsu shekarunta 8 ne amma sun tafi da sauran biyun wadanda don ita Najimatu ta gama Sakandire, tana makarantar koyan aikin jinya ne. Hasana da Husaina ko duk suna SS-1 ne za su SS 2.

“Bayan komi ya lafa ne sai muka nemi taimako daga mutanen gari don mu samu mu kai Babanmu asibiti, inda muka samu kaishi asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, kafin Allah yayi mishi cikawa.Su kuma ’yan uwana ba mu san inda suke ba har sai bayan da ‘yan sanda suka samu nasarar kwato su.”

Hajiya Husaina ita ce matar Alhaji Mustafa ita ma tana daga cikin wadanda maharan suka ganawa azaba a lokacin da suka fado gidan nasu, kuma ita ma ta bayyana wasu abubuwan da ta ganewa idanuwanta a lokacin da maharan suka shigo cikin gidan nasu, ta ce: “A gaskiya na ga tashin hankalin da ban taba ganin sa ba a duniya kuma ina rokon Allah da ya kare kowa daga irin wannan yanayin, domin ba su yi mana a hankali ba. Kuma ban zaci cewa zan kawo yanzu ba, saboda yadda na ji suna zubar da harsashi kai ka ce yaki ake yi tsakanin kasa da wata kasar don, haka abin sai wanda yake wajen. Ina kira ga gwamnati kan don Allah gwamnati ta kara zabura wajen taimakon rayukan jama’arta, kuma ta inganta maganar tsaraon ko ma samu mu rinka barci kuma ina rokon jama’a da su taya mu rokon Allah ya kubuto min da yarana guda biyu da suke hannun wadancan mutane kuma na ga kokarin ‘yan sanda wannan shi ya sa ina masu fatan Allah ya tsare mu baki daya”

Har wa yau, binciken jaridar LEADERSHIP A Yau ya bankado cewa wadanda suka aikata wannan mummunar barnar dauke suke da manyan makamai, wadanda sun fi karfin wanda rundunar ‘yan sanda ke rike da su, dalilin da ya sa su ka ci karfin su ‘yan sandar da suka kawo dauki a lokacin afkuwar lamarin.

Bincike ya nuna cewa baya ga shugaban ‘yan bangan, Malam Mustapha da suka harba akwai ‘yan sanda guda biyu dukkansu suna asibiti rai ga hannun Allah. Saboda a lokacin da su ‘yan sandar suka shigo anguwar ba su san cewa maharan sun zuba mutanensu ba a kan hanyar da ke zuwa wannan anguwar, hakan ta sa suka sami nasarar tula wa motar ‘yan sanda ruwan albarusai. Wata majiyar tamu ta ce, saboda rugugin wutar da maharan suka yi a yankin ya sa babu wani makwabcin da ya iya ko motsi balle ya leko ya ga abin dake faruwa .

Alhaji Shehu Abbas Sarkin Zuburi shi ne sarkin anguwar da lamarin ya faru, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu, kuma har ya nuna damuwarsa kwarai da gaske. Ya yi fatan Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan barna.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP. Muktar Husaini Aliyu, ya tabbatar da mutuwar shugaban kungiyar ’Yan Bangan ta Jihar Kaduna, Malam Mustafa, sakamakon harbin da masu garkuwa da jama’a suka yi masa a gidansa da ke Unguwar Katsinawa a garin Shika, karamar hukumar Giwa, cikin Jihar Kaduna.

Kakakin ya bayyanawa manema labarai cewa: “A halin yanzu, jami’anmu dake yankin Giwa sun kwato ‘yan matan da maharan suka yi garkuwa dasu, bayan karon-battar da aka yi.”

ASP Mukhtar ya ce; “Sakamakon arangamar, masu garkuwar sun jikkata dan sandanmu guda daya, wanda kuma a halin yanzu yake kwance a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika.”

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shugan ’Yan Bangan daga bangaren jami’an gwamani da sauran mutanen gari.

SendShareTweetShare
Previous Post

ILIMI A KANO: ’Ya’yan Talakawa Ne Kadai Ke Zuwa Makarantun Gwamnati A Jihar Kano

Next Post

Zunuban Gwamna El-rufai Ga ’Yan Jihar Kaduna

RelatedPosts

Amin

Yadda Ta Kaya A Taron Tunawa Da Malam Aminu Kano Karo Na 19

by Muhammad
1 day ago
0

Mun Gamsu Da Yadda Aka Tsara Taron Kan Tsaro Da...

AKCOE

Mataimakin Shugaba Kwalejin AKCOE Ya Zama Jakadan Zaman Lafiya A Nijeriya

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Mustapha Ibrahim, Mataimakin Shugaban Kwalijin Ilimi ta Aminu Kano...

Allah

An Roki Al’umma Su Dogara Ga Allah  

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai, Alhaji Bello Otunba wanda yake daya...

Next Post

Zunuban Gwamna El-rufai Ga ’Yan Jihar Kaduna

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version