Connect with us

LABARAI

Mahara Sun Sake Kashe Mutane 12 A Zamfara 

Published

on

Duk da sasanci da sulhu da Gwamnatin Jihar Zamfara ke yi karkashin jagoran Kwamishinan ’Yan Sanda Usman Nagogo, wasu maharan da ba su aminta da sasancin ba sun yi wa Unguwar Yabo a cikin karamar hukumar Tsafe dirar mikiya, inda su ka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, su ka tarwatsa garin bayan sun kashe mutane 12.

Malam Lawal Mustafa, mazaunin Unguwar Yabo ne, wanda ya shaida wa manema labarai cewa, da idanunsa ya ga gawa 10, sai kuma wani da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, ya ga gawa biyu a yashe a bakin fita garin.

Lawal Mustafa ya kuma kara da cewa, “maharan bayan sun kashe mutane kuma sun tarwatsa garin, sun yi awon gaba da shanu da tumakai, kuma yanzu haka mutane biyu na asibitin Tsafe kwance, daya kuma ya na asibibitin Yariman Bakura da ke Gusau.”

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar wannan harin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP. Muhammad Shehu.

SP Shehu ya tabbatar da cewa, mutane hudu ne maharan su ka kashe, kuma wadannan maharan sun fito ne daga hanyarsu ta zuwa Jihar Katsina kuma tuni rundunar ta tura jami’anta zuwa Unguwar Yabo, don cigaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.
Advertisement

labarai