Mahara Sun Sare Kan Maigadin Gidan Danmajalisar Imo

Watanni Biyu

Daga Idris Aliyu Daudawa

 

‘Yan bindiga da sanyin safiyar ranar ce suka kai hari gidan dan majalisar Jihar Imo Ekene Nnodumele a Ebenato, Awo Idemili, cikin karamar hukumar Orsu, suka sare kan mai gadin, daga bisani kuma suka sa ma gidan wuta.

Ekene Nnodumele dai yana wakiltar mazabar Orsu  a majalisar Jihar Imo.

Su dai ‘yan bindigar sun je har kauyen tsohon babban mai shari’a na kasa kuma kwamishinan shari’a Cyprain Charles Akaolisa, wadanda duk a unguwa  daya suke.

Daidai lokacin da ake hada shi wannan labarin majiyar tamu bata samu damar tuntubar shi jami’in hulda da jama’a na rundunar ba, Bala Elkana, wanda aka ce ba za a samu ganin shi ba.

Amma kuma  mataimakin Nnodumele Mista A. Nwadikwa, wanda ya tabbatar da aukuwar shi al’amarin, ya bayyana cewar su ‘yan bindigar sun yi ta harbe- harbe a gidan da sassafe, kafin su kai ga kashe shi maigadin.

Da akwai karar harbe- harben wadanda su ‘yan bindigar suka yi, jiya da dare kamar yadda dai shi Nwadikwa ya bayyana.

Exit mobile version