Khalid Idris Doya" />

Mahaukaci Ya Kashe Daliban Firamare Biyu A Ogun

Daga Khalid Idris Doya

A ranar Litinin ne wani da ake zargin yana fama da tabin hankali ya kashe wasu daliban Firamaren Saint John’s Anglican Primary School da ke Ogodo a jihar Ogun.

Su biyu mace daya na miji daya, daliban dukkaninsu ‘yan kasa da shekaru hudu sun gamu da ajalinsu ne a sakamakon sharba musu adda da muhaukacin ya yi.

Rahotonnin sun zo cewar mahaukacin ya shigo habarar makarantar ne daga dajin da yke kusa da makarantar dauke da sharbebeyar adda a tattare shi inda ya iske daliban a lokacin da suke yin karin kumullon samun abun jefawa a bakin salati da sauran daliban.

Muhaukacin dai ya arci na kare wajajen karfe 11:15 na safiya bayan da ya kammala aikata mummunar ta’asar tasa. A sakamakon sararsu da wannan addar, muhakacin ya bar daliban cikin jinni kafin kiftawa da bismilla.

Wata majiya ta shaida mana cewar wannan makarantar babu kofar kullewa domin tantance mai shigowa.

Kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya ta bayyana cewar iyayen daliban sun hanzarta yi wa makarantar kwanya domin kwashe ‘ya’yansu cikin gaggawa, inda kuma jami’an tsaro suka fantsama gudanar da binciken su kan lamarin.

A hirarsa da manema labaru a garin Abeokuta, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mr Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.

Oyeyemi, har-wa-yau, ya kuma kara baiwa ‘yan jaridan karin bayani kan hakan har ma da sunayen daliban da suka mutu a sakamakon farmakin da muhaukaci ya kai musu a makarantarsu, daliban kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan ya shaida su ne Mubarak Kalesowo da kuma Sunday Obituyi, dukkaninsu dalibai ne da basu haura wa shekaru hudu ba, kuma suna ajin karamin aji ne na neman ilimin firamaren.

Kakakin ya ce “Lamarin ta auku ne da misalin karfe11:30 na safe, a lokacin da daliban suke yin hudun karin kumullo na rana. Yaran suna kan yin wassaninsu,”

“Mutumin wadda muke tsammanin daga cikin daji ya fito, ya cakwami dalibai biyu kuma sun mutu, nan take ya fita da dan Karen gudu,”

“Wadda ya yi kisan ana tsammanin mahaukaci ne, mun nemi jin bayanin ko shi haifafen wannan wajen ne, amma har zuwa yanzu ba mu samu amsar hakan ba,”

“Mun dana tarkokinmu domin mu tabbatar da kamo shi. Maganar da mu zamu gamsu da ita shi ne, sai mun kamosa mun kaisa ga likitoci su ne kadan za su tabbatar mana da cewar shi mahaukaci ne ko kuma ba mahaukaci ba ne,”

Ya kara da cewa, “Ina tabbatar muka za mu kama shi, yanzu haka da na ke magana da ku, shugabanmu da ke kula da yankin da kuma DPO na Abigi dukkaninsu sun tashi tsaye zuwa wannan yankin domin ganin yadda za a yi a kamo wannan. don haka za mu tabbatar da kamo shi,” In ji Mai magana da yawun ‘yan sandan.

Exit mobile version