Jamil Gulma" />

Mahaukacin Kare Ya Ciji Mutane Goma A Kebbi

Kimanin mutane goma ne suka hadu da iftila’in cizon wani mahaukacin kare da yammacin ranar Larabar da ta gabata a anguwoyin ‘Yar mahauta, ‘Yar aduwa zuwa anguwar Danmagwaro da ke garin Argungu a cikin jihar Kebbi.
Malam Sani Abubakar Danmanga wanda ke zaune a anguwar yarmahauta wanda kuma yar sa mai suna Sa’ida Sani mai kimanin shekaru biyar da haifuwa ya bayyanawa wakilinmu da cewa duk da ya ke a lokacin da abin ya faru yana wani gari da ake kira Lailaba da ya ke ba nisa sai nan take ya iso garin Argungu ya zarce zuwa babbar asibiti inda ya tarar da kanen sa tuni ya kawo ta kuma har soma yi mata aiki duwawu inda karen ya cijeta.
Malam Sani Danmanga ya ce suna nan tsaye kafin a kammala aikin ‘yar sa sai ga shi ana shigowa da mutane daya bayan daya har mutum bakwai mazajen da mata.
Hakazalika Malam Bashar wani malamin tsangaya da ke da almajirai a anguwar Danmangwaro ya bayyanawa wakilinmu da cewa jiya ne da yamma yara suna karatu a kofar gida sai suka ga mahaukacin karen ya nufo su baki bude daga nan sai suka watse sai ya nufi Nasiru dan kimanin shekaru goma sha biyu da ke kwance a gefe ba shi da lafiya ya cije shi a kafa daga nan ya kuma yi gaba zuwa wajen gari aguje daga nan sai aka dauke shi zuwa asibiti inda a lokacin da suka he sun tarar asibitin ta cika da mutane da aka kawo ‘yan uwansu.
Dokta Emma (Ima) shi ne Shugaban babbar asibitin ta Argungu ya shedawa wakilinmu da cewa an kawo mutane takwas ranar Laraba sannan kuma da safe ranar Alhamis kuma aka sake kawo wata yarinya mai suna Hafsatu Sani daga anguwar Matanfada mai kimanin shekaru biyar, ya kuma ce tuni an yi musu aiki an sallame su.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Shugaban karamar hukumar mulki ta Argungu Honarabul Musa Muhammad Tungulawa amma wayarsa a kashe inda daga bisani ya sami zantawa da Alhaji Tukur Dalijan Shugaban sashen albarkatun gona na karamar hukumar mulkin ta wayar tarho, ya kuma tabbatar masa da faruwar al’amarin kuma ya ce bisa ga al’ada karamar hukumar mulki ce ke daukar nauyi idan aka samu wani iftila’i mai kama da wannan hasali ma ta kan sayi magunguna ta ajiye amma dai a halin yanzu ba ta iyawa.
Ya kara da cewa bisa ga doka kuma a duk lokacin da kare ya ciji wani mutum ko wata dabba wannan hakkin mai kare ne ya sauki nauyin maganin barnar da karen ya yi idan ba shi da lasisi amma idan yana da lasisi to akan dauko al’amarin a matsayin kaddara hasali ma saboda haka ne hukuma ta ce kowa ya rinka kai Karen sa asibitin dabbobi a yi masa allura a kowace shekara.
Ya kuma yi kisa ga al’umma da a duk lokacin da suka lura da saresarin hauka ga wani kare to mutanen anguwar su yi gangami su kashe shi.
Majiyoyi daga anguwar matan fada sun tabbatar da cewa yan sanda daga Argungu tuni sun yiwa anguwar dirar mikiya inda suka harbe mahaukacin karen.

Exit mobile version