Mahaukacin Kare Ya Kashe Mutum Biyu Hade Da Jikkata Wasu A Garin Dambam

Daga Khalid Idris Doya, Bauci

A ranar Juma’a 1/9/2017 (ranar sallah) ne al’ummar garin Dambam da ke jihar Bauci suka fuskanci aukuwar wani iftila’I, inda wani mahaukacin Kare ya bazama cikin gari inda ya yi ta cizon jama’a. Karen wandaya yi ta yin cizon kan mai uwa da wabi ba tare da ware babba ko yaro a yayin da yake kan cizon nasa ba. Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu nan take, hade da jikkata wasu adadi masu yawa, inda a halin yanzu suke rai kwaikwai, mutu-kwaikwai a gadon jinya.

Jin aukuwar wannan lamarin wakilinmu ya fantsama don jin yadda lamarin ya auku, inda ya tattauna da wasu mutanen da abun ya shafa, Abdullahi Muhammad Tudun Wada mazaunin garin Dambam, wanda ya kasance ganau ne kan lamarin ya shaida mana cewa: “Muna zaune a ranar sallah babba, tun da yammaci bayan sallar La’asar kawai sai muka ga Kare ya shigo garinmu ya kama cizon jama’a. cizon da ya yi na farko a kan idonmu shi ne cizon da ya yi wa wata yarinya ‘yar gidan Malam Haruna, mai suna Shafa’atu. Abu kamar wasa sai muka sake jin ya ciji wani a wata unguwar kuma, kafin kiftawar ido ya garzaya wani yankin ya sake cizon wani ko wata. A lokaci guda sai ka ji Karen ya yi cizo a unguwar Gwangwalo, mintu biyu, ba sai aka ji ya sake cizo a Kandar, sai kuma aka sake jin ya ciji wani yaro a Tudun Wada, daga nan kuma sai aka ce an ganshi ya gangara unguwar Kunkuru, wannan abun shi ne ya baiwa kowani mutumin garin mamaki, ya za a ce cikin kankanin lokaci kasa da minti 10 kare daya ya karade unguwanni da dama da cizon jama’a”.

Abdullahi Dambam ya ci gaba da shaida min cewa, nan take al’umman garin suka dauki matakin kashe dukkanin wani Karen da suka yi arbu da shi .“Shi mai girma Hakimin garin Damban Alhaji Idris Musa Sulaiman ya bada umurnin cewa, dukkanin wani Karen da ke da lasin to a daure sa, duk kuma karen da aka gani a waje to a kashesa. A bisa haka ne mutanen gari suka fito da sanduna, adduna da sauran makamai irin su gariwo da adda domin neman mafita, inda suka kashe karnuka da daman gaske sai dai babu tabbacin a cikin karnukan da aka kashen akwai wanda ya yi wannan ta’addancin ba, domin mun ga lokacin da ya fito daga unguwar Bayi, karnukan da suke wajen suka rufasa a guje ya fita baa sake ganinsa ba. Amma ka san shi Karen hauka ba wai wani ganesa ake yi taido ba”. inji Abdullahi Dambam

Da yake mana bayani kan ta’asar da mahaukacin Karen ya yi a karamar hukumar mulkin Dambam din ya ce, mutane biyu nan take sun mutu har lahira a sakamakon cizon na kare. “Ya zuwa yau dai muna da alkaluman mutane goma ne wannan Karen ya yi musu cizo a lokaci guda. Nan take a kan idonmu kuma yara biyu sun rasu a sakamakon cidon Karen, an kuma yi musu sallah kamar yadda addini ya gindaya. Majinyatan an kaisu asibitin Azare ne domin nema musu taimakon gaggawa”. In ji Ganau

Dakta Haruna Zakari shi ne Darakta da ke kula da dabbobi na ma’aikar gona da albarkatun kasa.Ya shaida yadda suka samu lamarin, “Idan aka samu cizon muhaukacin kare irin haka, koda an kashe sa akwai wasu abubuwan da muke bukata a cikin kansa domin gwaje-gwaje don tabbatar da shi Karen yana dauke da cutar haukan ko bai da shi, amma da ma’aikatanmu suka isa wajen, sun tararsa al’umman sun kashe Karen kuma an farfasa mai kai, an farfasa masa jiki babu wani abun da zamu iya cira daga jikinsa don bincike amma mun yi amfani da wadanda Karen ya ciza don bincike”. In ji sa

Ya bayyana cewar irin wannan lamarin fa babbar matsalace wacce take bukatar kulawar gwamnati cikin gaggawa. “Kare ya ciji mutane goma a rana daya gaskiya ba karamin abun tada hankali ne ba.Mun nemi taimakon gwamnati kan lamarin kusan magungunan da za a yi amfani da su wajen yin rigafin karnuka din yana da wahalar samu daga can Damban, Ya zama dole a nema daga cikin Bauci domin karnukan da suke yankin na Damban da kauyukan wajen suna da yawan gaske don haka akwai bukatar gwamnati ta taimaka wa ofishinmu na can da kuma karamar hukumar don shawo kan matsalar”. In ji Daktan

Exit mobile version