Bala kukkuru legas">

Mahauta Na Cigaba Da Samun Nasara A Legas – Sarkin Fawa

Sarkin Fawan Kasuwar Mile 12 Intanashinal Market a cikin garin Legas, Alhaji Usman Illela ta karamar hukumar Illela da ke cikin Jihar Sakkwato, ya bayyana cewa, shi da sauran mahauta na unguwar Mile 12 da Jihar Legas bakidaya su na cigaba da samun nasarori a wajen gudanar da harkokin sana’ar fawa a Legas da kewayanta.

Sarkin Fawan na unguwar Mile 12 ya yi wannan tsokaci ne a ofis dinsa da ke unguwar Mile 12 jim kadan bayan tashi daga taron su na mahauta da su ka saba yi a duk karshen wata, domin tattaunwa a bisa kan yadda za su kara nemo hanyoyin da za su cigaba da kawo cigaban sana’ar fawa tare da zuwan akasin hakan.

Ya cigaba da cewa, babu shakka daga ’yan shekarun baya kadan da su ka wuce zuwa yanzu sana’ar fawa ta kara samun daukaka, idan a ka yi la’akari da irin yawan mutanen da su ka samu rufin asiri a cikinta.

A cewarsa, “wadansu sun gina gidaje, wadansu sun sayi motoci da sauran makamantansu. Da fatan Allah ubangiji ya cigaba da zaunar da Nijeriya lafiya.”

Ya kara da cewa, a kan haka ya ke kara kira ga mahautan kasar su rike gaskiya komai dacinta, musamman a lokacin da su ke gudanar da harkokin kasuwacinsu na yau da kullum.

Sarkin Fawan ya cigaba da tsokaci a bisa ga irin cigaba da ya ke ganin kasuwar ta na Mile I2 ta ke kara samu a halin yanzu, ya na mai cewa, babu shakka kasuwar a halin yanzu ta na kara samun cigaba, domin kuwa ta samu shugaba tsayayye, wanda shuwagabannin bangarorin kasuwar su ke goya ma sa baya a wajen gudanar da ayyukan cigaban kasuwar.

Ya cigaba da cewa, “a halin yanzu idan ka shiga kasuwar za ka ce ka shiga kasuwar Amerika ko London ko kasuwar wata kasa makamanciyar irin wadannan kasashen da su ka cigaba, kuma shugaban kasuwar ta Mile I2 ya hada kawunan ’yan kasuwar gabadaya da sauran kabilu mazauna yankin bakidaya. Shi ya sanya al’ummar Hausawa da sauran kabilu mazauna kasuwar su ke ta sanya ma sa albarka a game da wannan al’amari.

Daga karshe ya ce, ya na mai isar da sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ’yan uwa da abokan arziki da kamfanin Jaridar LEADERSHIP bisa ga rasuwar shugaban kamfanin, Sam Nda-Isaiah, tare da fatan Allah ubangiji ya ba su juriyar wannan rashi da Nijeriya ta yi bakidaya.

 

Exit mobile version