Daga Bala Kukkuru, Legas
Malam Ma’azu Talatar Mafara wanda shi ne jami’in hulda da jama’a na kungiyar mahauta shanu kwatar Agege, Jihar Legas, ya koka game da yadda gwamnatin jihar take neman ta maida su gugar yasa a kasuwsar mayankar shanu.
A cewarsa, akwai kungiyogi da dama na mahauta masu neman abinci da gwamnatin ta dakatar da su a kasuwar daga baya kuma ta dawo da su amma cewa bangaren Hausawa a kasuwar wai ba za ta dawo da su ba alhali Hausawan ne ma karfin kudaden shigar da kasuwar ke samu.
Ya kara da cewa, hatta masu acaba Hausawa da kan fito da jamaa daga cikin mayankar shanun, gwamnati ta ce kar ta sake ganin wani mai babur ya shiga cikin kasauwar.
Bugu da kari, Ma’azu ya ce a kan wannan dokar ce suke kira ga gwamnatin Jihar Legas da ta duba wannan matsi sannan ta sassauta musu domin samun daidaito.