Daga Balarabe Abdullahi, Zariya
‘Yan ƙungiyar mahauta ta Nijeriya, reshen Ƙaramar Hukumar Sabon gari a Jihar Kaduna, sun zaɓi Alhaji Adamu Ibrahim Chigari a matsayin shugaban ƙungiyar, wanda zai jagorance ta nan da shekaru huɗu masu zuwa.
A jawbinsa wajen ƙaddamar da sababbin shugabannin, Iyan Zazzau, Alhaji Bashari Aminu,ya jawo hankalin shugannin, da aka zaɓa da su yi jagoranci mai, adalciga waɗanda suka zaɓe su, tare kuma da riƙe amanar ƙungiyar, kamar yadda kundin tsarin mulkin ta ya tanadar.
Iyan Zazzau wanda Ɗan Amar na zazzau ne,Alhaji Abubakar Alhaji ya wakilta,ya ce riƙe amanar shugabanci, da kuma yin adalci ga waɗanda ake mulka,su ne za su kai mai mulki ga yin daraja ga waɗanda yake mulka, kuma su yi kewarsa ko da bayan mulkinsa ne ko kuma bayan rayuwarsa a nan gaba.
Sabon shugaban da aka zaɓa, Alhaji Adamu Ibrahim Chigari,da farko ya nuna matuƙar jin daɗinsa, da yadda suka ba shi damar ya shugabanci wannan ƙungiya.Ya ce da yaddar Allah mai mowa mai komai, zai ba su kunya ba, saboda sun zaɓe shi ne domin sun san, zai masu jagoranci na gari.
Saidai kuma Alhaji Adamu ya ƙara jaddada ba fa zai cimma nasarar shugabancinsa ba, sai duk wani mahauci da ke Ƙaramar Hukumar Sabon gari,ya ba shi goyon baya da kuma addu’o’in, da za su tallafa ma sa ya sami sauƙin fuskantar ayyukan da aka ɗora masa. Ya yi fatan hakan zai tabbata.
A dai jawabinsa ya yi alƙawarin yin gyare-gyre,domin inganta sana’ar fawa da kuma tsabtace nama,sai batun tsaro da bin dokokin ƙungiyayar da fito da hanyoyin da za su haɗa kan ma su sana’ar fawa da kuma ganin an ciyar da sana’ar fawa gaba a ciki da wajen jihar Kaduna. Alhaji Adamu ya ƙara da cewar,daga lokaci zuwa lokaci, za a riƙa yin taron kowa da kowa, domin sanar da jama’a halin da ƙungiya ke ciki, tare da karɓar shawarwarin ‘ya’yan ƙungiya da kuma sanya iyayen ƙungiya a gaba a duk lokacin da buƙatar haka ta taso a nan gaba.
Sabon shugaban mahauta na Ƙaramar Hukumar Sabon gari,Alhaji Adamu Ibrahim Chigari,ya kammala da cewar,nan gaba kaɗan duk duk wata magana da ta shafi yankar dabbobi, za a koma abatuwa, za a yi haka ne, in ji shi, domin samun tsaro ta ko wanne fanni.
Wannan taron ƙaddamar da sababbin shugabannin ƙungiyar mahauta, ya sami halartar shubannin ƙungiyar mahauta na Jihar Kano da babban shugaban ‘yan kasuwa na kasuwar Sabon gari,Alhaji Ibrahim Mai Gwal da kuma ‘yan siyasa da suka fito daga sassan ciki da wajen jihar Kaduna.