Fasto Yohanna Y.D. Buru" />

Mahimmancin Taimako

Ikorinthi Yawa 12:28: “Kuma Allah ya sanya mutane a cikin ekklisiya, na farko manzani, na biyu annabawa, na uku masu – koyaswa, liana ayuka, musa-iko, kana baye baye na warkaswa, taima kai, dadarun mulki harsuna iri-iri.”
Allah Ubangiji mai kowa da kmai, ya sanya mutane daban daban a cikin Ekkilisiyanasa. Allah Ubangiji ya bads bayebaye ga kristan duniya domin zuwa ga dayantuwar imani da sani dan Allah da kuma aikin hidima, domin ginin jikin Kirista.
Manzo Bulus ya ruwaito cewa: “Ya kuma bada wasdansu su zama manzanni; wadansu, Annabawa; wadansu, masu – wa’azin bishara; wadansu, makiyaya da masu – koyarwa, domin kamuntawar tsarkaka, domin aikin hidima, domin ginin jikin Kirista; har dukanmu mu kai zuwa dauyantuwar imani da sanin Dan Allah, zuwa tsawon cikar Kirsita.” (Afidawa 4: 11–13).
Allah Ubangiji cikin hikimarsa ya bada baye-baye a cikin ekklesiya domin karfafawa da cingaban Ekklesiyasa. Hailama Yesu Almasihu ya yi baye-baye ga Ekklsiya domin aikin hidima, domin ginin jikin Krsiti, domin kai zuwa dayantuwar imam da sanin dan Allah zuwa cikakken mutum, zuwa misalign tsawon cikar Kirista.
Haka kuma ruhu maitsarki ya bada nasa bayebayen dadom daban domin hidimomi a cikin ekklesiya Allah Ubangiji ko das hike bayebayen daban daban da kuma ayukan daban-daban, amma ruhu guda ne. (Romawa 12: 4–8) da mu Ikorinthi yawa 12: 4–11).
Duk bayebayen da Ubangiji Allah, Yesu Almasihu da ruhu maitsarki suka bai Ekklesiya da kuma bil Adama. in mun koma ga littafin Ikorinthiyawa 12:28, a cikin wannan ayar zamu tarar da cilin bayebayen da Allah ya, bada tawurin Ruhu maitsarki zamu tarar da baisuwar “Taimako”.
Watau baiwar “Taimako” wata babbar baiwa ne ga Ekklesiya Allah domin taimallon jina. wannan baiwan taimako na da mahinaci sosai domin taimakon kowane irin mutum ba tare da nuna bambancin kabila, jinsi, yare ko addini. Wannan kyakyawan baiwa ce ga Ekklesiya domin taimakeniya ga kowane irin poil Adama.
Domin da haka ko kai Kirista ne ko muslmi ne ko mabambantan addinai ne baiwan taimako baya zaban wanda za a taimaka. a’a’. wannan baiwar taimako da Allah Ubangiji ya bai wa Ekklesiya shi ya sa Kiristan duniya na taimaka wa kowane jinsin mutane.
Wannan bai kan taimako ne mostsa Kiristan duniya da krsita na taimakon kowane mutum ba tare da nuna bambancin addini ba.
Mahimmancin wannan baiwan ta yi mai shi ne dalilin da Kirista na taimakon mukwabtansa Musulmi a wanna lokaci na hidiman addini watau Azumin ramathan ko wasu hidimomi da bokukuwa. baiwan taimako, na kara dankon zumunci, ta kan karfafa kyalyawan zumunci, kyantata zamantathewa da makwabta da kuma mabambantar addinai.
Baiwar taimako kan inganta fahimtan juna da kuma iganta zaman lafiya da juna a kowane mataki. Baiwan taimako, ya kan rege nau’in talauci tsakanin alumma, ya kuma inganta tattalin arzillin al’umma.
Taimako babbar baiwa ce ta aikin Allah domin idar da sakon allah tawurin yin alheri. Baiwan taimako, wata hanya ne na bishara ko idar da sokon Allah. watau baiwan taimako watau aikin Allah Ubangiji bambanta masu imani da marasa imani tawarin basu baiwan taimako domin su daukaka shi ta wurin taimakon juna domin shi mai jin kai ne da rahama ga hallitarsa.
Kowane irin baye-baye da Allah ya bai wa Ekklesiyansa domin taimakon juna ne da sauran bil adama. Kuma Allah Ubangiji zai tamabaye mu abinda muka yi da bayebayen day a bamu a rahan tashin mattatu. Ubangiji Allah zai tamabye me kuma zai sharanta mu a ranar matuka bamu yi amfani da baiwar da ya ba mu.
Matuka Kiristan duniya ya nuna bambanci a kan taimakon jama’a zai tarar da fushin Allah tashin mattatu. Son kai da kuma kin taimallon mabukata babban laifine wurin Allah Ubangijinmu. taimako ga mabukata shine cikon addini, domin addini na koyarwa da taimako juna ne, domin imani juna ta karfafu. A cikin bin Allah a kowane mataki taimako.
Mahimmancin taimako bata misaltuwa domin baiwan ne da Allah ya baiwa Ekklesiyarsa, domin taimakon mutane. Domin da haka kristan duniya ya farka daga barci ya kuma yi aikin taimako domin cigaban al’umma.
Kiristan duniya dole ne ya taimaki kowa da kowa domin daillin kenan da Allah ya ba mu baiwan. A yi amfani da baiwa “Taimako” don hakan al’umma domin sunan Ubangiji shi sami daukaka.
Shalom! Shalom!! Shalom!!!

Exit mobile version