Mahukunta Ba Su Daukar Kwararan Matakai Don Kare Kwararowar Hamada —Mai Teku

Alh. Ibrahim Salisu da akafi sani da Mai Teku Farm dake cikin Jihar Kaduna sannen matashi ne a jihar waje sana’ar  shuka yayan itatuwa. A hirar sa da ABUBAKAR ABBA, ya yi bayani yadda yanayin sanyi ke shafar yayan itatuwa, da barazanar karanchin ruwa da itatuwan ke fusknata, yadda ‘yan farauta ke janyo illa wajen kona dazuzzuka, barazanar hamada da sauran su.

Bisa la’akari da yanayin sanyi da ake ciki a yanzu, wanne alfanu ko rashin sa yake janyowa itatuwa?

Kwarai kuwa, jiki ma ya kan chknza ballantana itatuwa, domin duk wanda ya kalli itatuwa a wannan lokacin zai ga suna yin kakkaba. A cikin itatuwa kadan ne suke son yanayi sanyi, kamar a cikin mutane akwai wadanda ba su son yanayin sanyi haka itama rayuwar itatuwa take. Ina ganin a cikin yayan itatuwan da suka fi shahara wajen son sanyi itace Tuffa wato Apple sai uma Inibi, amma sauran itatuwan suna fuskantar barazana, mussaman wadanda suke a sahara da kuma a yankin Arewa maso Gabas.

 

Mene ne ra’ayin ka a kan yadda Majalisar Dinkin Duniya UN take yin kokari wajen sanyawa a shuka itatuwa don kare kwarararowar Hamada a Nahiyar Afirka?

Abu ne mai kyau domin shi ne muke wayar wa da kan mutane a kan mahimmancin yin hakan a kulkum, sai dai, duk wasu yayan itatuwan da take sanya wa a shuka bata neman masana domin ana kokarin yaki da kwararowar Hamada, amma itatuwan da take sanya a shuka a dazuzzuka kanana ne idan kuma aka yi la’akari wannan lokaci ne na rani rashin ruwa zai iya zama barazana ga yayan itatuwan.

A kullum Babban Bankin Duniya ya na yin magana a kan samarwa da ‘yan Adam ruwan da zai sha inaga itatce, in har aka ci gaba da haka, Hamada za ta ci gaba da kwararar a cikin nahiyar mu. Shawarar da muke baiwa UN a kullum ta nemi masana kwararru don su bata shawara a kan irin yayan itatuwan da ya kamata ta sanya a shuka a dazuzzukan dake nahiyar Afirka musamman a yankin Arewa maso Gabas na kasar nan.

A kalla a yankin Arewa maso Gabas in za a shuka itatuwa su kasance sun kai zurfin muta uku. Akwai bukatar mahukunta mussmman a kasar nan su zauna da masu sana’ar renon ‘yayan itatuwa a tattuna dasu a kan tadda zasu samar da yayan itatuwa mita biyu ko uku da za a kai daji a shuka, sai dai ruwa shi ne babbar matsala dake shafar dukkan fadin jihohin kasar nan. Ba wai ruwan da za a sha ba akawai bukatar a samar da Dam-Dam a ko wacce jiha. Hamada ta na tunkarar nahiyar mu da kusan mita shida kyma ga dukkan alamu babu wani kwakwaran mataki da ake dauka don kare kwararowar Hamada.

 

Yadda sare itatuwa a cikin dazuzzuka yake kara zamowa ruwan dare a kasar, kana ganin akwai sakaci a bangaren gwamnati?

Gaskiya akwai sakaci, musammana a bangaren malaman gandun daji, in ka lura a nan Kaduna basu cuka damuwa da shiga cikin daji ba, kullum suna a kan titina ne suna lura da masu shigowa da itacen, yanzu kuwa da dare ne ake yin fasakaurin sa ta barauniyar hanya zuwa cikin gari. Ba wai muna kalubalantar masu yin sana’ar bace domin sana’a ce suke yi, amma ya kamata gwamnati ta tashi tsaye ai suna biyan gwamnati haraji akwai kuma masu yi ta haramtacciyar hanya.

 

Ina mafita a ra’ayin ka dangane da yadda ‘yan farauta ke kona dazuzzuka, musamman a lokacin hunturu?

Ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakai, kamar yadda gwamnatin el-rufai ta yi a kokacin da ta karbi mulkin jihar ta nuna zasu yi yak da kwarariwar Hamada da kuma kona dazuzuka a jihar, mussmman ganin cewar jihar Kaduna UN bata sanya ta a jerin wadanda suke fuskantar barazzanar Hamada ba, lokacin da yazo ya yi kokarin sayen yayan itatuwa da za a shuka har miliyan uku don a nunawa UN cewar gwamnatin a shirye take wajen yaki da kwararowar Hamada a cijin jihar duk da yawan sare itatuwan da ake yi a cikin dazuzzukan dake cikin jihar zuwa wasu jihohi, a saboda hakan akwai bukatar a shuka wasu yayan itacen da yawa a jihar.

Akwai kuma bukatar a janyo mysamman Sarakuna don kare kwararowar Hamada da kara kare mafarauta shiga dazuzzuka don yin farauta ta hanyar kona dazuzzukan.

 

Exit mobile version