Daga Abba Ibrahim Wada
Rahotanni sun bayyana cewa mahukuntan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea sun fara gajiya da uzurin da kociyan ƙungiyar yake ba su sakamakon rashin nasarar da suke samu a ‘yan kwanakin nan.
Chelsea dai ba ta fara kakar bana da ƙafar dama ba, inda ta yi rashin nasara a wasannin uku ciki har da wasan farko wanda ta yi rashin nasara a hannun Burnley har gida, sai kuma wasan da Manchester City ta lallasa ta da kuma wasan da sukayi rashin nasara a satin da ya gabata a hannun Crystal Palace da ci 2-1.
Sai dai shugabannin gudanarwar ƙungiyar ba su yarda da dalilan da Conte yake ba su ba na ciwon da ‘yan wasansa suke zuwa.
Sannan Conte ya yi ƙorafin cewa wasanni sun yi yawa a ƙasar ingila; sam babu hutu, wanda hakan yake nuna cewa ba zai iya lashe gasar Firimiya ba, saboda a kakar wasan da ta gabata, ƙungiyar ba ta buga gasar Zakarun Turai ba, wanda hakan ya sa ba su buga wasanni da yawa ba.
A kwanakin baya dai Conte ya ce ba zai dade yana koyarwa a waje ba, saboda yana son ya koma gida domin cigaba da koyarwa, kuma tuni ƙungiyoyi irinsu AC Millan sun fara zawarcinsa.