Connect with us

DAGA NA GABA

Mai Babban daki Hasiya Bayero: Gwarzuwarmu Ta Mako

Published

on

Hajiya Hasiya Bayero ita ce mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Kano Marigayi Alhaji Ado Bayero. Hajiya Hasiya mace ce jaruma mai hakuri da son baki mace ce mai kyauta da biyayya matuka da iya tafiyar da jagorancin al’umma, sannan kuma jajirtacciya wajen tarbiyyar iyali. Babban misali shi ne sarkin Kano na Yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya tashi a hannunta ya sami tarbiyya da kulawarta inda yau ya zama abin koyi.

Tarihinta:
An haifi Hajiya Hasiya a birnin Kano a unguwar Darma. Mahaifinta shi ne Muhammadu Kabir wanda asalinsa Babarbare ne , ‘ya’yansa kan kira shi da Abba Kabiru. Abba Kabiru zuriyar gidan sallaman Kano ne su ne jama’ar sarki masu kula da bindiga da harba ta. Abba Kabiru ya kai har matsayin mai-ta-fari a harkar buga bindiga (wato ya kai matsayin shugaban masu buga bindigar sarki a zamanin sarkin Kano Abbas wanda ake wa lakabi da Maje Nasarawa.
Mahaifiyar Hajiya Asiya ita shuwa arab ce mutuniyar Wadai Fallomin Chadi gaba da kasar Borno.Lokacin da aka kawo ta Kano ba ta jin harshen Hausa sai dai yaren Shuwa. Sunanta Umma Kaltume amma ana kiranta da Tatiye . Abba Kabiru da Tatiye sun haifi yara da yawa amma guda hudu ne suka tsaya ragowar duk sun rasu. Hajiya Asiya ana kiranta da Asabe sannan a gidan sarki ana kiranta da Mai turare wanda ta samu wannan lakabin ne a lokacin wasan gauta a gidan sarki ta fito a matsayin sarkin musulmi Mai Turare.
Tun asali Abba Kabiru yana zaune ne anan kusa da gidan sarkin Kano amma lokacin da za a yi aiki don fadada masallacin cikin gari na fadar sarki sai sarki y aba su gida a unguwar Darma inda nan unguwar ta Darma a nan aka haifi Hajiya Hasiya. Abba Kabiru ganin unguwar Darma ta yi masa nisa da fada sai yay i ta rokon sarki kan a sauya masa gida. Sarki sai ya ba shi gida a Maraba( Durumin Iya) ana yi wa mutanen unguwar maraba kirari da maraba ta rabe da sarki. Anan unguwar ta maraba mahaifan Hajiya Hasiya suka rasu. Mahaifin Hajiya Hasiya ya rasu tun zamanin sarkin Kano Abbas Maje Nasarawa. Inda mahaifiyarta Umma Kaltume ta rasu a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Bayero. Hajiya Hasiya tana tunawa da iyayenta a kowanne lokaci tana yawan yi musu sadaka haka ko kyauta ta yi da bakinta take cewa Allah ya jikan iyayenta ya gafarta musu.
Daga cikin makusanta sa’ointa dda suka taso tare akwai Aishatu matar Yari sun taso tun kuruciya a gidan sarkin Gaya sai Uwar soron sarkin Kano Sunusi Khadija Wayo da Adama Uwar kuyangin gidan sarki da Karimatu (Hakama) matar sarkin Hatsi Muhammadu da sauransu. Hajiya Hasiya ta lakanci sarauta kwarau da gaske da dukkan al’amuranta a mataki daban-daban har ta taka babbar daraja da mai babban daki. Ko lokacin da Alhaji Muhammadu Sunusi ya zama sarkin Kano Hajiya Asiya ce ta je ta koya wa uwar soro wayo irin ayyukan da uwar soro take yi tsakaninta da sarki da kuma jama’ar cikin gida. Sannan ta nusar da ita kyawawan halayen mu’amala da jama’a. Hajiya Asiya ta san wannan halaye ne saboda zamanta uwar soron sarki Alhaji.

kuruciyarta A Gidan Sarkin Gaya:
Lokacin da yayarta Saudatu (kankani) ta isa aure sai aka aurar da ita ga Shamakin Fulani Sa’adatu Gandi matar sarkin Gaya Malam Muhammadu wanda ya yi sarauta tsakanin shekara ta 1904-1921 inda aka kai ta gidan sarkin Gaya Muhammadu tare da jama’arta a ciki akwai shamakinta da matarsa da kanwarta Asabe (Hajiya Hasiya). Hajiya Hasiya ta yikuruciyarta a garin Gaya tare da yayarta
A garin Gaya ta fara karatun allo ta yi kawaye sosai a lokacin kuruciya a garin Gaya ta san wurare da dama a garin saboda a lokacin sune yara da ake aika.A rayuwarta tana yawan cewa tana kaunar garin Gaya saboda anan ta budi ido. Hajiya Hasiya sun ci gaba da zama a wajen Fulani Gandi ita da yayarta kankani har lokacin da Allah ya karbi ran sarkin Kano Abbas Maje Nasarawa (1903-1919). Lokacin da ‘yarsa Fulani Gandi ta tafi Kano daga Gaya domin ta’aziyyar mahaifinta, ta tafi tare da jama’arta da kankani da Asabe. Lokacin da Fulani Gandi za ta koma Gaya sai aka karbi Asabe aka bar ta a wurin sabon sarki. An nada sarki Kano Shehu wanda ake wa lakani da dan tsoho ana ce masa dan tsoho saboda sai da ya tsufa ya samu sarautar Kano. Barin Hajiya Hasiya a gidan Sarkin Kano kawayenta sun damu sosai sun yi kuka sun yi kewarta. A wannan lokacin Fulani Gandi tana da shekara goma sha hudu.
Hajiya Hasiya ta samu rayuwarta a cikin gidan sarki a wannan lokacin tana da kimanin shekara goma sha hudu da haihuwa. Saboda haka ba a saka ta duk wasu ayyuka na wahala kamar jan ruwa a rijiya kamar yadda sauran matan gida ke yi sannan bugu da kari tana da farin jini saboda haka ma sarki ma ba ya son ta yi aikin wahala. Haka ta zauna har zamanin sarkin Kano Usman na biyu har Allah ya yi masa rasuwa. Bayan Sarkin Kano dan tsoho ya rasu sai aka nada Ciroman Kano Abdullahi Bayero babban dan Sarkin Kano Abbas a matsayin sarkin Kano. Daga nan ta koma hannun sarki Abdullahi Bayero. Ba a hada Hajiya Hasiya da wata uwar daki ba mai kula da ita ta zauna ne ita kadai sai abin da Sarki ya ba ta umarni. Daga baya da uwar Soro ta dauki danta sai ta rinka mu’amala da uwar soro kamar uwar dakinta.
Hajiya Hasiya mai babban daki ta haifi ‘ya’ya hudu tare da sarkin Kano Abdullahi Bayero. Ga sunayensu kamar haka :-
Muhammadu Kabiru (Barde kerarriya) sai Ado Bayero ( marigayi Sarkin Kano) sai Rukayya (Dudu) sai Salamatu. Mai babban daki ta zauna a soron sarki tare da sauran abokan zamanta. Hasiya ta kyautatawa sarki da kyawawan halaye. Sarki yana alfahari da ita saboda kyawawan halayenta da kyautatawa kadan daga abinda take yin a dadadawa sarki akwai duk lokacin kayan marmari kamar gyada sabuwa takan dafata ta bare ta zuba a mazubi mai kyau ta ba yaro ya kai wa sarki haka tana yin kwadon zogale da mandako haka lokacin rogo da gurjiya ko data. Sarki yana jin dadin wannan sosai saboda jin dadin wannan sarki yakan yi mata kyautar kudi ko goro ya zuba a kwanon a kawo mata. Duk rayuwar Hajiya Hasiya ta yi ta ne tare da sarakuna a gidan sarakuna ta fara daga gidan sarkin Gaya zuwa mashahuriyar masarautar Kano inda ta yi haife-haifenta. Ta zauna da sauran jama’ar gidan sarki lafiya.
Bayan rasuwar sarkin Kano Abdullahi Bayero Hajiya Hasiya ta ci gaba da zama a cikin gidan sarki ta zauna tare da Umma Uwar soron sarkin Kano Abdullahi Bayero sun zauna a Unguwar farin gida a cikin gidan sarki. Hajiya Hasiya mace ce mai son turare matuka hatta takardun kudin da suka fito daga hannunta kamshin suke yi haka nan tufafinta duk wanda ya san kamshin turaren da ta saba sawa zai shaida cewa kudin ko kayan daga hannunta suka fito. Kafin ta rasu sai da ta zabi turaren da za a mata sutura da shi.

Zamanta Uwar Soro:
A shekarar 1963 Alhaji Ado Bayero ya zamo sarkin Kano sai Hajiya Hasiya suka dawo unguwar Jarkasa da zama a gidan da aka yi wa mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero a gidan da aka yi wa sarki Ado auren fari. Sun zauna na dan lokaci kadan kafin a gama ginin mazaunin babban daki a Unguwar gwangwazo. Bayan an kammala sun dawo da zama Gwangwazo. Ta zama mai babban daki tana da shekara 58.

Daga Cikin Yara Maza Da Mata Da Ta Rike Akwai:-
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Fulani Salamatu (Goggo) matar Sarkin Gaya da sauransu.

Rasuwarta:
Hajiya Hasiya Mai Babban daki ta rasu ranar laraba 15 ga watan Yuni a shekarar 1990 misalin karfe goma saura minti sha biyar na dare . Allah ya jikanta da gafara, amin.

An ciro wannan tarihi ne a cikin littafin tarihin Mai Babban daki Hajiya Hasiya Bayero mai suna ‘Rumfa Sha Shirgi’, wanda Hajiya Salamatu Kabiru Bayero (matar Sarkin Gaya) ta wallafa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: