Daga Rabiu Ali Indabawa,
Rundunar ‘yan sanda reshen Jihar Ondo ta cafke wani mai gadi da ke aiki a gidan mai na S.A. da ke garin Ondo, Abiodun Osuntimehin, bisa zarginsa da hannu da yi wa ofishin fashi.
Bayanai sun nuna Abiodun shi ne ya shirya fashin da aka yi a gidan man. An ce an kashe wani gadi yayin aiwatar da fashin, inda daga baya kuma suka sace Naira miliyan biyu.
Da yake gabatar da wanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Bolaji Salami, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi gaban kotu.
Ya ce, “An kashe wani mai gadi kuma an sace kimanin Naira miliyan biyu daga wurin ajiyar, amma abin farin ciki shi ne mutumin da ya aikata wannan mummunan aikin nan da nan masu bincikenmu suka kama shi, wanda bai bai tabuka komai ba yayin da ake kokarin kama shi.
“Abiodun Osuntimehin, mai gadi tare da wannan kamfani, shi ne ya jagoranci aikata hakan; ya amince da aikata laifin kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da shi gaban alkali domin yanke masa hukunci daidai da laifin da ya aikata,” inji shi.