Connect with us

Uncategorized

Mai Hakuri Yakan Dafa Dutse

Published

on

Dabi’ar dan’adam ce son kai wa ga nasara da cikar buri cikin kankanin lokaci, kuma ba tare da wata wahala ba. Fatanmu a kullum bai wuce samun biyan bukata cikin gaggawa ba. Masu hakuri da juriya da jajircewa a kan hadafinsu ba su fiye burge jama’a ba. Mukan yi musu kallon wahalallun da bai kamata su zamo abin koyi a wurin mu ba.

Dole ne a kan duk mai son kai wa ga nasara ya bai wa kansa tarbiyyar hakuri da juriya. Ba wani ingantaccen sakamako da ake samu matukar aka yi aiki cikin garaje da rashin natsuwa. Hausawa na cewa “gaggawa ba ta kunu”.

Kyakkyawan shiri da tsari da kuma kokarin tanadar kayan aiki su ne makaman da ya kamata mutum ya rike a duk lokacin da ya daura niyyar aiwatar da wani abu.

Ta hanyar jajircewa da dauriya ne mutum zai iya kau da duk wani tarnaki da shamaki da suke kan hanyarsa ta zuwa ga nasara. Domin a kowane lokaci nasara tana samuwa ne in aka daure aka yi hakuri aka yi naci sosai.

Bambancin da ke tsakanin wadanda suka ci nasara da kuma wadanda suka fadi yana tattare da irin kokari da dagewarsu a lokacin da suka fuskanci kalubalen rayuwa.

Wasu mutanen, da zarar sun hadu da wata matsala, sai ka ga sun tsaya cak! A maimakon su yi tunanin mafita. Ya kamata ne a ce sun yi amfani da hikimarsu da basirarsu wajen kawar da wannan tarnakin, ba wai su watsar da shirinsu ba. Ba sukan yi wani kazar-kazar ba, kudurinsu yakan zamo rarrauna, sakaci da nuna halin ko in kula ya zamo jiki a gunsu. Irin wadannan mutanen da kyar suke tsinana wani abin arziki a rayuwarsu.

Rayuwa a kullum fadi- tashi ce tun daga farkonta har zuwa karshenta. Hakuri da juriya su ne ma fi ingancin guzurin da mutum zai tanada a wannan tafiyar mai matukar hatsari da sammatsi. Nasara a wannan fagen dagar ta jarumai ce, tsayayyu kyam! Wadanda ba su san wani abu wai shi gudu ko mika wuya ba, ko sau nawa za su samu tangarda da tuntube, za su mike ne kawai su ci gaba da fafutukarsu, har su ga sun kawar da dukkan wani shinge da ya gitta tsakanin su da samun nasararsu.

Dakta Marden (wani masanin halayyar dan’adam) ya bayyana rawar da wahalhalun suke takawa wajen gina halaye da dabi’u; a inda yake cewa: “Kamar yadda ake amfani da wuta a makera wajen samar da kayan aiki masu inganci, haka jarabawowin rayuwa suke kyautatawa da inganta halaye da dabi’u.”

“Kokari wajen ganin an kai ga wani matsayi na yabo yana da matukar amfani. Ko da mutum bai kai ga wurin da yake hari ba, to zai samu karfin zuciya da azamar sake fuskantar wani sabon kalubalen na rayuwa.”

Masanin falsafar nan dan kasar Jamus, Hegel, yana cewa: “Ba a yi duniya don sharholiya ba, an yi ta ne don kai wa ga muradi. Duniya ba fage ne da ake kafa tarihi a cikin ruwan sanyi ba, ana kafa tarihi ne lokacin tsanani da wahala.”

Haka nan wani masanin yake cewa: “Kamar yadda wasu tsirran ba a jin kamshinsu, sai an murtsika su, to haka nan wasu mutanen bajintarsu da kwazonsu, ba sa bayyana sai sun fada cikin wahala.

“Ma fi muni daga cikin abubuwan da ake koya wa mutum shi ne duk wani abu da ke kai shi ga raggonci da lusaranci; domin a dukkan yanayi, asara da kuma wahala su ne malaman da suka fi kowane malami hikima wajen koya wa mutum hankali. Suna sa mutum ya zama mai karfin hali, suna horas da shi, su sa masa tarbiyya da wayewa. Suna koya masa hakuri da juriya, suna gyara masa tunaninsa da kuma yadda yake kallon al’amura.”

Nasarar da ta fi kowacce inganci da kyau da dadi da faranta rai ita ce, wadda aka same ta bayan an yi kyakkyawan nazari na dalilan da suka jawo asara da faduwa, kuma aka yi amfani da darussan da aka samu. Thomas A. Edison, mutumin da ya kirkiri kwan lantarki, an ce ya jarraba hanyoyi kusan dubu goma (10,000) kafin ya kai ga nasarar samar da kwan. Da aka ce masa amma fa ka bata lokaci, sai ya ce, “ba wani bata lokaci, sai dai na kara sanin dubban hanyoyin da in an bi su ba za a iya samar da kwan lantarki ba.”

Nazarin dalilan da suka sa aka yi asara yana sa mutum ya gano matsaloli da maganinsu. Yana buda wa mutum mahangarsa ta yadda hanyar kai wa ga cikar buri za ta bayyana rangadadau a gabansa.

Himma da kokarin wasu mutanen sukan bayyana ne lokacin da suka yi arangama da wani dabaibayi ko tarnaki a kan hanyarsu ta kai wa ga muradinsu. Mutane da dama ba sa gane bai war da Allah ya yi musu, sai bayan sun auka cikin matsala. A kokarinsu na neman mafita sai ka ga sun yi wata bajinta da jarumta, wadda ko su kansu ba su taba zaton za su iya yin makamanciyarta ba.

Wadannan mutane masu karfin hali ba sa yanke kauna, kuma ba sa sako-sako da himmarsu da azamarsu da kokarinsu har sai sun ga sun tatso wani darasi mai amfani daga hantsar wahala da jarrabawa. Ba sa taba sare wa su watsar da aniyarsu, duk rintsin da suka shiga, kuma duk wahalar da suka fuskanta, sai sun ga sun kai ga cikar burinsu. Duk lokacin da suka kama wani aiki, za ka samu suna yinsa cikin kuzari da kumaji, ba sa saduda su mika wuya har sai sun kai ga abin da suke hako. In kuma an yi rashin sa’a, hakarsu ba ta cim ma ruwa ba, to tabbas za ka samu sun kara kintsa wa sosai, sun fuskanci wannan abin a karo na biyu. Haka za su yi ta yi, ba za su hakura su bari ba, har sai sun kayar da wannan matsalar.

Kuskure ne don mutum ya samu matsala a kan hanyarsa ta neman isa zuwa ga bukatarsa, ya ce ba zai kara gwada sa’arsa ba, don tsoron jin kunya da kuma izgilin da mutane za su yi masa. Abraham Lincoln, tsohon Shugaban kasar Amurka, ya sha faduwa a zabubbuka daban-daban kafin daga karshe a zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Duk wani ci gaban zamani da ake ganin an samu, wadanda wani lokacin ma ba ma ganinsu a bakin komai, to da farko an dauke su ne a matsayin gagarau wadanda ba za su taba yiwuwa ba. A wancan lokacin duk wanda ya ce zai gwada yinsu, to sunansa mahaukaci, abin yi wa izgili da shammaci.

A shekara ta 1859, Edwin L. Drake, ya zama abin yi wa dariya da izgili da tsokana don ya yi tunanin cewa za a iya samun mai a karkashin kasa. To, amma yanzu fa? Masu tsukakken tunani sun yi kokarin hana Wright Brothers kera jirgin sama, don suna ganin ba yadda za a yi ‘tsuntsun karfe’ ya iya tafiya a sama. To, amma ai ka ga yanzu ba ka bukatar fada wa kowa cewa ‘tsuntsun karfe’ abu ne mai yiwuwa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: