Mai Kungiyar Kwallo Ta Leceister City Ya Mutu Sakamakon Hatsarin Jirgi

An tabbatar da mutuwar mai kungiyar kwallon kafa ta Leicester City a hadarin da jirginsa ya yi a wajen fillin wasan kungiyar bayan kungiyar ta tashi daga wasan da sukayi 1-1 da kungiyar Westham..

Mista Bichai Sribaddhanaprabha, da wasu ma’aikata biyu da matukin jirgin da kuma fasinja guda ne suka mutu bayan jirgin ya fado jim kadan da barinsu fillin wasa da aka buga wasan firimiya a daren ranar Asabar.

Shaidu sun ce jirgin mai saukan ungulu ya yi ta watangariri a sama kafin daga bisani ya fado da karfi inda hayaki ya turnuke ko ina a harabar filin wasan na King Power dake birnin na Leceister dake kasar Ingila.

Dubban mutane ne su ka yi dafifi inda suka ajiye furannin da kyallaye domin nuna alhini a kan abinda ya faru ga kungiyar wadda ta lashe kofin firimiya a shekara ta 2016.

Mr Bicahi, ya mutu yana da kimanin shekara 60 a duniya, inda kuma ya bar mace guda da ‘ya’ya hudu.

Ya sayi kungiyar ta Leicester City ne a 2010, kuma a karkashinsa ne kungiyar ta lashe gasar firimiya a shekara ta  2016.

Kungiyar Leicester, ta bayyana Mr Bichai a matsayin mutumin kirki wanda ya ke matukar kula da iyalinsa.

Kungiyar ta ce ‘ A karkashin jagorancinsa, gabaki dayan ‘yan kungiyar kansu a hade  yake ba bu wani bambanci a tsakaninmu, don haka wannan mutuwa ta sa babban rashi ne a gare su da ma magoya bayan kungiyar.

 

Exit mobile version