Fitaccen Malamin nan na Gombe mai arangama da aljannu ya cire su daga jikin duk wanda ya gamu dasu, wato Malam Sani Yakubu Mai Rukiya Zahra, ya jinjina wa Gwamnan Gwambe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a kan yadda ya shushuka bishiyoyi a fadin Jihar.
Malamin wanda yake gudanar da harkokin shi na abin da ya kira “Yaki da aljanu” a anguwar Yalengurza na garin Gombe, ya yaba wa Gwamnan ne a lokacin wani hira da ya yi da manema labarai a Zahrar Rukiyar shi a makon da ta gabata. A cewar shi, bishiyoyi suna da muhimmanci tun kaka da kakanni, domin sune ginshikin taimakon alumma saboda haka inji shi, “Dole muyi farin ciki akan yadda mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya yake ta dassa itatuwa a cikin garin Gombe da kewaye, kuma jinjina mishi ya zama dole, musamman ire-iren mu masu waraka da al’ummah”.
Malam Sani Yakubu sai ya shawarci jama’a da su daina sassare bishiyoyi, yana mai cewa, su za su bada gudunmawar su wajen kare bishiyoyin daga masu sara ko tuttuga su, yana mai karawa da cewa duk wata bishiya tana da amfani a jikin dan Adam, domin garkuwa ne daga cuttutuka da kuma kariya ga gine-gine.
Malamin wanda yace an haife shi ne a garin Potiskum ta Jihar Yobe, ya ce yana da yara sama da dari da suke gudanar da ayuyyukan shi a Jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Kano da kuma nan Gombe, baya ga dimbin wadanda ya horar cikin shekarun da yayi yana rukiyar shi.
Ya bayyana cewa, shi a halin da yake ciki, a makance yake gudanar da harkokin rukiyar sa amma idan Allah ya kai wa’adin aikin shi, zai koma mai gani tangaran kamar kowa, yana mai cewa, a duk tsawon shekarun da yake harkar rukiyar shi, bai taba samun wani miskila ba, sai dai daukaka sabooda a cewar shi, “mu rukuyar mu taimako ne ga al’ummah”.
Daga karshe, Malam Sani Mai Rukiya Zahra, yayi kuka ga Gwamna Inuwa Yahaya, da ya tallafa wa masu kananan sana’oi domin su kara bunkasa harkokin su, su kuma baiwa matasa aikin yi, yana mai adu’a da Allah ya taimaki Gwamna da Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Shehu Abubakar Shehu a kokarin su na samar da zaman lafiya a fadin Jihar Gombe.