Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Mai Shari’a Fatima Sulaiman Takuma

by
5 years ago
in FITATTUN MATA
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Ko-Kun-San

Barista Fatima Suleiman Takuma tana ɗ aya daga cikin Alƙalai a babbar Kotun Jihar Neja. Ta kasance tsohuwar Shugabar Ƙungiyar Alkalai Mata ta Ƙasa da ƙasa (International Federation Of Women Lawyers (FIDA).  ’Yar asalin Jihar Neja, ta fito ne daga wani gari da ake kira Takuma.  Mahaifinta tsohon ɗ an jarida ne amma daga baya ya zama gogaggen ɗ an siyasa. Ta fara aiki ne tun  daga matakin akawu kafin ta kai wannan matsayi na babbar alkali.

Fatima Takuma babban burinta dai shi ne ta ga tana kare ‘yancin gajiyayyun, wannan dalilin ne ya sanya ta shahara ta kuma yi fice, domin kuwa ta yi amfani da damar da Allah ya ba ta wajen ƙwato wa gajiyayyu da marasa galihun da ake zalunta ‘yancinsu, wannan matakin da ta ɗ auka ya cilla likafarta ya kuma sanya ta cikin fitattun matan da suka yi zarrara.

Labarai Masu Nasaba

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

 

  • Shin wace ce Fatima Suleiman Takuma?

‘Yar asalin jihar Neja ce, amma ta yi zama a garuruwa da dama kasantuwar canjin wajen aiki da aka yi ta yi wa mafahinta. Fatima ta yi karatu tun daga matakin ƙasa har zuwa sama, inda ta samu zarafin kammala digirinta na farko a Jami’ar Abuja. Fatima tana daga cikin ɗ aliban farko a wannan jami’ar daga 1990 zuwa 1995. Haka kuma ta halarci Makarantar Horas da Lauyoyi (Law School) inda ta kammala a shekarar 1996.

Da farko ta fara karatun ta na digiri ne a Jami’ar Maiduguri a Fannin Shari’a (LLB), sai dai ba ta kai ga kammalawa ba a can sai ta canza zuwa Abuja sakamakon ɗ awainiyar aure da na yara, inda zirga-zirgan ya yi mata yawa.

Fatima ta fara aiki a shekara ta 1987 tun daga ƙaramin muƙami har ta kai zuwa matakin mataimakiyar babbar Alƙali, haka kuma ta zama babbar Alƙali a Babbar Kotun Jihar Neja.

Shahararta da gogewarta sun ba ta dama har ta riƙe muƙamin shugabar ƙungiyar Lauyoyi Mata ta ƙasa da ƙasa daga 2013 zuwa 2017. Wannan muƙamin ya yi matuƙar taimaka wa Fatima domin kuwa ta samu zarafin taimaka wa mata ‘yan uwanta sosai a yayin da take rike da wannan muƙamin da ma sauran masu gajiya da mabuƙata. Babban burinta shi ne ta ga tana taimakon al’umma a ɓ angaren shari’a musamman gajiyayyu.

Fatima Suleiman Takuma ta kansace mace kamar maza, domin kuwa ba ta wasa ko sakaci da kwato haƙƙin mata musamman waɗ anda aka zalumta, ta sha kare haƙƙin mata da gajiyayyu sosai, wannan taimakon nata ma ya sake cilla likafarta ya yi sama, inda ta samu sanuwa a lunguna da kuma saƙuna.

Kasantuwarta mace mai sha’awar ɓ angaren shari’a ta maida hankali sosai wajen tsayawa domin koyon gami da yin shari’a kamar yadda ya kamata domin kuwa ta taso da sha’awar fannin ne tun tana ƙarama.

Burinta dai ya fara cika ne tun daga lokacin da ta zama Lauya kuma babban alkali a jihar Neja, amma Barista Fatima tana sha’awar ta kasance Babbar Alkali ta Kotun ɗ aukaka ƙara da ke ƙasar nan. Hakan kuma bai wuce ta ci gaba da kare haƙƙin marasa galihu ba.

Daga cikin shari’un da Fatima ta taɓ a yi wanda kuma ya taimaka mata wajen kasancewa fitacciya a jiharta akwai wata yarinya da waɗ ansu ɓ atagari suka yi wa fyaze a garin Kwantagora. Bayan an yi mata fyaɗ e sai aka bar ta a yashe, inda aka ɗ auka ma ta rasu. Nan take ta haɗ a tawaga suka nufin asibitin da aka kwantar da ita.  Mai shari’a Fatima ta nemi bayanin daga wajen likitan da ke duba ta inda ya bayyana cewa suna da ƙarancin kayayyakin aikin da za su yi mata cikakken bincike.

Wannan dalilin ne ya sanya mai shari’a Fatima ta canza mata asibiti, inda suka kai ta asibitin IBB domin ceto rauwarta cikin gaggawa.  A can ne aka gano cewa ɓ atagarin sun ɗ ura mata maganin da ake ba doki ne da hakan ya sa ta faɗ i sumammiya har na tsawon lokaci.

Waɗ anda suka aikata mata hakan ’ya’yan masu hannu da shuni ne. Sun yi ƙoƙarin ganin an kwantar da batun amma mai shari’a Fatima ta yi tsayin-daka wajen tabbatar da an shigar da ƙara a kotu da kuma ɗ aukaka ƙara har sai da aka hukunta su. Wannan ɗ aya ne daga cikin matakan da suka sanya mai shari’a Fatima ta sanu ta kuma samu lambar jinjina sosai daga wajen al’ummun da abun ya shafa.

Kasantuwar a kowani lokaci burin mai shari’a Fatima ke nan kare haƙƙin gajiyayayu da marasa galihu, hakan ya sa ta yanke shawarar ɗ aukan ɗ awainiyar wannan yarinyar har sai da komai ya daidaita.

 

Khalid Idris Doya daga Bauchi

Kidrisdoya200@gmail.com

07069724750

 

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

ALƘALAMI: Masomin Gini Daga Tushe

Next Post

Raino Da Tarbiyya: Ko Akwai Wasu Haƙƙoƙin Maigida Bayan Haihuwa?

Labarai Masu Nasaba

Maryam Ibrahim Shettima

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: Sarauniyar Arewa ‘Yar Gwagwarmayar Kishin Kasa Da Al’umma

by
10 months ago
0

...

Hajiya Kyari Joda

Bunkasa Rayuwar Al’umma Shi Ne Babbar Buri Na – Hon. Hajiya Kyari Joda

by
10 months ago
0

...

Hafsat

Hafsat Ganduje Garkuwa Ga Mijinta A Fannin Shimfida Ayyuka

by
11 months ago
0

...

Farfesar

Adenike Osofisan: Mace Ta Farko Farfesar Kimiyyar Kwamfuta A Nahiyar Afrika

by
1 year ago
0

...

Next Post

Raino Da Tarbiyya: Ko Akwai Wasu Haƙƙoƙin Maigida Bayan Haihuwa?

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: