Abba Ibrahim Wada" />

Mai Tsaron Ragar Bayern Munchen Ya Tuba

 

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Sben Ulreich ya bawa kungiyar da magoya bayan kungiyar hakuri sakamakon kuskuren da yayi kuma ya yi sanadiyyar zura musu kwallo a raga a wasan da suka fafata a ranar Talatar data gabata.

Bayern Munchen da Real Madrid sun fafata wasa na biyu na gasar cin kofin zakarun turai zagayen wasan kusa dana karshe a filin wasa na Santiago Barnabue dake birnin Madrid sai dai Real Madrid din ce tasamu nasara a wasan.

Tun farko dai a wasan farko Bayern Munchen din ce tasha kashi daci 2-1 har gida a watan daya gabata sai kuma wasa na biyu da suka buga 2-2 wanda hakan yasa Madrid tasamu tikitin zuwa wasan karshe na gasar.

Kwallon da Tollisco ya bugowa mai tsaron ragar ne shi kuma ya tawo zai dauka sai daga baya ya gane cewa bazai iya daukar kwallon da hannu ba kuma yayi kokarin buge kwallon da kafarsa amma kuma ya fadi sai Benzema yaje ya buga kwallon raga ce tabawa Real Madrid kwallonta ta biyu kafin daga baya kuma James ya farkewa Bayern din.

Mai tsaron ragar yace yayi bakin ciki da basu samu damar zuwa wasan na karshe ba domin sunyi kokarin yin hakan amma kuma hakan bai kasance ba saboda kuskuren da yayi.

Yaci gaba da cewa yana bawa shugabannin kungiyar da yan wasa da kuma magoya bayan kungiyar dake fadin duniya hakuri bisa wannan kuskure da yayi kuma yajawo musu fita daga gasar.

A karshe yace sunso zuwa wasan karshe saboda sun cancanta idan aka kalli irin kwallon da suka buga  a wasan.

Mai tsaron ragar dai ya bugawa kungiyar wasanni 44 a wannan kakar sakamakon rashin mai tsaron ragar kungiyar Manuel Neur wanda yake jiyya a yanzu haka.

Exit mobile version