Abba Ibrahim Wada" />

Mai Tsaron Ragar Kasar Ivory Coast Ya Yi Ritaya Daga Buga Kwallo

Tsohon mai tsaron ragar kasar Ivory Coast, Boubacar Barry yayi ritaya daga buga kwallon kafa bayan daya shafe shekaru 22 yana buga kwallo a matakai daban daban a duniya kuma ya samu nasarori.
Barry, wanda yafara buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta ASEC Memosas dake kasarsa ta haihuwa ya bugawa kasarsa ta Ibory Coast wasanni da yawa ciki har da wasannin cin kofin duniya dan a nahiyar Africa.
A shekara ta 2001 ne yafara bugawa kungiyar kwallon kafa ta Rennes ta kasar Faransa wasa kafin daga baya kuma ya koma kungiyar Beberen ta kasar Belgium a shekara ta 2003 kafin kuma daga nan ya sake barin kungiyar zuwa kungiyar Lokeren a 2007.
Ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta tricolores wasanni 239 inda ya zura kwallo daya a raga sannan kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin kalubale na kasar Belgium sau biyu a shekara ta 2012 da kuma 2014.
“Daga yau na ajiye kwallon kafa wadda na shafe shekaru 22 ina fafatawa kuma zan koma mai koyarwa kamar yadda na tsara a rayuwa ta saboda haka ina godiya da jinjina ga masu bibiyar wasanni na” in ji Barry
Yaci gaba da cewa “Ba karamar nasara nasamu ba a rayuwa ta tun daga lokacin da nafara buga kwallo domin na buga wasanni da dama kuma nasamu nasarori a kungiyoyin dana bugawa wasanni a tsawon rayuwa ta”
Boubacar Barry dai ya wakilci tawagar kasarsa ta haihuwa wato Ivory Coast a wasanni 86 tun daga lokacin da yafara wakiltar kasar kuma yana daya daga cikin wadanda suka taimakawa kasar ta lashe kofin nahiyar Africa a shekara ta 2015.

Exit mobile version