Wani rahoto ya bayyana cewa, sakamakon karuwar farashin mai a kasuwan duniya wanda a yanzun haka gwamnatin tarayyar Nijeriya na kayyade farashin mai ne biya yadda kasuwa ta ka, hakan zai iya yuwuwa a kara dawa da tallafin mai a Nijeriya. Tun daga ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar 2020, farashin mai bai sake karuwa ba a cikin kasar nan, a yanzu farashin danyan mai a kasuwan duniya ya tashi daga dala 41.51 zuwa dala 51,22 ga kowacce gangan mai tun daga ranar 31 ga watan Disamba. ‘Yan kasuwan mai sun yi tsammanin samun sabon farashin mai ganin yadda danyan man yake bunkasa a kasuwan duniya. Gwamnatin tarayya ta rage naira biyar daga cikin farashin mai a ranar 14 ga watan Disamba, sakamakon gyara da aka yi a bangaren man fetur.
Karamin ministan mai Timipre Sylba ya bayyana cewa, tun daga watan Satumba na shekarar da ta gabata, gwamnatin tarayya ta dakatar da kayyade farashin mai a Nuijeriya. Ya kara da cewa, ana saka farashin ne bisa yadda kasuwa ta kayyade.
Gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai ne dun a watan Maris ta shekarar 2020, bayan rage farashin mai daga naira 145 zuwa naira 125 ga kowani lita daya na man fetur. An dai ci gaba da rage farashin man har zuwa watan Yuni. ‘Yan Nijeriya sun ci gaba da fuskantar karin kudin mai na tsawan wata hudu, inda ya fara tashi tun daga naira 121.50 zuwa naira 123.50 a watan Yuni, sannan ya tashi daga naira 140.80 zuwa naira 143.80 a watan Yuli, haka kuma ya tashi daga naira 148 zuwa naira 150 a watan Agustan, a watan Satumba ya tashi daga naira 158 zuwa 162, daga karshe ya tashi daga naira 163 zuwa 170 a watan Nuwambar shekarar 2020.
A kasuwan mai na duniya kuwa, danyan mai ya karu zuwa kashi 35 tun daga ranar 13 ga watan Nuwamba. Inda a ranar Juma’a kowacce gangar mai ta kai dala 55.99 wanda ya karu na tsawan wata 11.
“Har yanzu akwai sauran burbushin tallafin mai, amma gwamnati ta karkashin kamfanin mai suna rufe lamarin,” kamar yadda shugaban ‘yan kasuwan mai na Nijeiya, Mista Mike Osatuyi ba bayyana wa manema labarai lokacin da ya zanta da su.
Ya bayyana cewa, a cikin watan Disamba farashin man ya kusa kai 180 ga kowacce lita daya. Ya kara da cewa, da wannan farashin danyan mai a yanzu, akwai tallafin mai wanda ya kai na naira miliyan 800 ga kowacce rana a cikin litar mai guda miliyan 40 wanda masu amfani da man suke saya. Ya ci gaba da cewa, saboda ‘yan siyasa suke cinye kudaden ne ya sa ba a so a kawowa ‘yan Nijeriya sauki wanda wannan lokacin ne ‘yan Nijeriya ke matukar shan wahala a bangaren mai.
Osatuyi ya ce, “amma ya kamata gwamnatin tarayya ta bayyana wa majalisar kasa tallafin da ake bayarwa a halin yanzu. Ya kamata a fada wa ‘yan Nijeriya za a koma lokacin bayar da tallafi. Saboda bashin da gwamnatin tarayya ta amso a wajen hukumar bayar da lamuni ta duniya da kuma Bankin Duniya akwai sharadin gyara bangaren mai, ina fatan gwamnatin tarayya za ta yi kokarin dakile matsalolin da ake fuskanta a yanzu.
“Idan an gyara bangaren mai yadda ya kamata, duk wadannan matsaloli ba za su dunga faruwa ba, amma akwai abubuwan da ke boyewa wajen gyara fannin mai a halin yanzu.” In ji shi.