Rahotanni na cewa wasu kasashe na kokarin shiga tsakani domin ganin Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bai wa shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Moden-Lumana Africa, wato Hama Amadou damar komawa kasar, bayan ya share dogon lokaci yana zaune a waje daidai lokacin da bangaren shara’a ke neman sa.
Amadou Salah, jigo ne a jam’iyyar ta Lumana, kuma yayin tattaunawarsa, AbdoulKareem Ibrahim Shikal ya tambaye shi ko akwai wani yunkuri mai kama da haka mai kama da haka, sai jigon ya amsa da cewa a halin yanzu sun sanya idanu don ganin yadda tattaunawar sulhun zata kaya.
A cewar Salah ida har kuma aka gaza cinma kyakkyawar matsaya a tattaunawar shiga tsakanin, sai a zuba idanu zuwa shekara ta 2021.