Mai Zamba Da Sunan Aljani Ya Sami Matsuguni A Gidan Yari

MATSAGUNI A GIDAN YARI

 Yanzu haka rundunar ‘yan sanda ke Birnin Zariya a jihar Kaduna, ta sami nasarar yin kamun kazar kuku ga wani mutum mai suna Suleman Abdulrahman day a kware wajen yin muryar Aljannu, ya na zambatar mutane a sassa daban-daban a jihar Kaduna.

Jami’in da ke gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifi a kotun majastare da ke Birnin Zariya, ya bayyana haka ga Alkalin kotun Barista Umar Bature, a lokacin day a gabatar da wanda ake zargi a gaban Alkalin.

Dan sandan ya ci gaba da cewar, wani mutum mai suna Malam Suleman Mohammed da ke gida mai lamba 34 a Unguwar Liman a Birnin Zariya ya kai karar wanda ake Zargi a wannan ofishi cewar wanda aka damke ya umurci wanda ya kai karar day a sayar da motarsa, ya kawo ma sa kudin zai yi masa addu’ar da zai sami kudi fiye da yadda ya ba shi kudin.

A cewar dan sanda mai gabatar da ma su laifi a wannan kotu, Malam Suleman Mohammed ya ba wanda ake zargi Naira dubu sittin da biyar da farko, amma day a ga bai sami biyan bukata ba, shi ne ya shaida wa ‘yan sanda, bayan ya ce ma say a kara ba shi naira dubu arba’in da biyar.

Wanda ake zargi ya ce wa mai karar da ya kai ma sa dubu arba’in da biyar, shi ne ya shaida wa ‘yan sanda wannan batu, a nan ‘yan sanda suka yi shigar manoma suka je inda wanda ake zargi ya ce a kai ma sa kudin, suka yi kamar suna yin noma a gonarsu, sai wanda ake zargi ya tsaya nesa da inda ya ce a kai ma sa kudin, suna ta waya da wanda ya kai kudin cewar ya na ganinsa, ya ce wanda ya kai kudin ba zai gan shi ba, domin shi Aljani ne.

Bayan Malam Suleman Mohammed ya aje kudin inda wanda ake zargi ya ce ya a je kudin, sai wanda ake zargi ya je zai dauka, a nan fa ‘yan sanda suka yi ma sa kofar-rago, suka dake shi a nan take.

Bayan ‘yan sanda sun kawo Suleman Abdulrahman da ke zaune a Layin Dattawa-Rigasa ofishinsu, suka yi ma sa wasu ‘yan tambayoyi, a cewar dan sanda mai gabatar da wadanda ake zargi a kotun, sai suka gabatar da shi a gaban wannan kotu, domin yanke ma sa hukumci.

Dan sanda mai gabatar da wadanda ake zargi a kotun ya ce, in zargin da ake yi ma sa, za a hukumta shi a karkashin dokoki ma su lamba 377 da kuma 307.

Bayan mai gabatar da wadanda ake zargi ya kammala bayani a gaban Alkalin kotun Barista Umar Bature, sai Alkali ya tambayi wanda ake zargi, cewar ya ji zargin da ake yi ma sa? Sai ya ce lallai ya ji, kuma ya aikata laifin da ake zarginsa das hi, amma sai ya ce, ya na rokon Alkali ya yi ma sa sassauci wajen yanke ma sa hukumcin laifin da ya aikata.

Alkalin kotun ya ce, tun da wanda ake zargi ya ki amincewa da cewar bai tsoratar da wanda ya kai kara ba, sai Alkalin ya ce za a ci gaba da binciken wannan zargi, amma tun day a amsa zargin ya zambaci Suleman Mohammed, a nan ta ke sai ya yanke masa hukumcin daurin shekara goma a gidan yari, ko kuma ya biya tarar Naira dubu dari biyu.

A karshe, Alkalin kutun Barista Umar Bature, ya umurci rundunar ‘yan sanda su ci gaba da binciken wanda aka yanke masa hukumci na batun tsoratar da Suleman Abdulrahman da ya ce bai yi ba.

Exit mobile version